Rudani Yayin Da ’Yan Bindiga Su Ka Hallaka Babban Mai Sarautar Gargajiya da Su Ka Yi Garkuwa da Shi
- Bayan ‘yan bindiga sun sace mai sarautar gargajiya a yankin Otulu a jihar Imo, daga bisani an tsinci gawarsa a bakin hanya
- Marigayin mai suna Eze Joe Ochulor an yi garkuwa da shi ne a ranar Asabar 25 ga watan Nuwamba
- Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Henry Okoye ya tabbatar da kisan mai sarautar inda ya ce za su kama wadanda su ka aikata hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Imo – ‘Yan bindiga sun hallaka mai sarautar gargajiya a yankin Otulu a karamar hukumar Ezinihite Mbaise a jihar Imo.
Marigayin mai suna Eze Joe Ochulor an yi garkuwa da shi ne a ranar Asabar 25 ga watan Nuwamba, cewar The Sun.

Kara karanta wannan
Ku kara hakuri, Tinubu na da shirin ciyar da kasar nan gaba, shawarin minista ga 'yan Najeriya

Source: Twitter
Yaushe aka hallaka mai sarautar?
Wata majiya ta tabbatar wa Punch cewa an tsinci gawar marigayin a bakin hanya a wani kauye da ke karamar hukumar Mbaise a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce:
“An hallaka mai sarautar gargajiya a yankin Otulu a karamar hukumar Ezinihite Mbaise a jihar Imo.
“An tsinci gawar mamacin a bakin hanya a karamar hukumar Mbutu a ranar Asabar da dare bayan sace shi da safiyar ranar.”
Mutanen yankin sun shiga tashin hankali saboda rashin sanin abin da ka iya biyo baya a yankin, cewar Chronicle.
Martanin 'yan sanda a kan kisan
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Henry Okoye ya tabbatar da kisan mai sarautar inda ya ce za su kama wadanda su ka aikata hakan.
Ya ce kwamishinan ‘yan sanda a jihar ya umarci jami’an tsaro su bazama don binciko wadanda su ka aikata wannan danyen aiki.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun bindige shugaban PDP har lahira a gaban idon matarsa, an fadi wacce ake zargi
Wannan na zuwa ne bayan hallaka wani shugaban jam’iyyar PDP da wasu ‘yan bindiga su ka yi a jihar.
Maharan sun bindige Chiedoziem Anyanwu a gaban idon matarsa bayan sun bukaci ganinsa.
‘Yan bindiga sun hallaka shugaban PDP
A wani labarin, wasu ‘yan bindiga sun bindige Chiedoziem Anyanwu a gaban idon matarsa bayan sun bukaci ganinsa.
Marigayin shi ne shugaban jam’iyyar PDP a yankin Ife/Akpodim/Chokoneze da ke karamar hukumar Ezinihitte Mbaise a jihar.
Asali: Legit.ng