Ana Tsaka da Jin Jiki a Najeriya, Sanata Yari Ya Ware ’Yan Zamfara 1000 Zai Tallafa Musu da Magani

Ana Tsaka da Jin Jiki a Najeriya, Sanata Yari Ya Ware ’Yan Zamfara 1000 Zai Tallafa Musu da Magani

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya kawo tsarin tallafawa marasa galihu da jinyar ciwon ido kyauta ba tare da biyan ko anini ba
  • An bayyana hakan ne a lokacin da Abdulaziz Yari ya kaddamar da shirin a jihar, inda ya ce mutum 1000 za a yiwa aiki a yanzu
  • Jama’a da dama na fama da ciwon ido a wannan zamanin, musamman duba da yadda kayayyakin fasaha ke kara shiga hannun jama’a

Jihar Zamfara - A ranar Asabar Sanata Abdulaziz Yari ya kaddamar da aikin jinya da tiyatar ido kyauta ga marasa lafiya 1,000 a yankin Sanatan Zamfara ta Yamma, Daily Nigerian ta ruwaito.

Yari, mai wakiltar Zamfara ta Yamma a majalisar dattijai, ya bayyana a yayin wani taro a babban asibitin Talata-Mafara, cewa cibiyar kula da ido ta Visions Savers ce za ta gudanar da aikin.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Kano, Bello, ya bayyana abu 1 tak da ke sa shi farin ciki a rayuwarsa

Yari zai taimakawa 'yan Zamfara wajen magance ciwon ido
Za a yi aikin yiwa 'yan Zamfara aikin ido
Asali: Getty Images

Yari wanda ya samu wakilcin tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar, Lawal Liman, ya ce hakan na daya daga cikin ayyukan gudunmawarsa ga fannin lafiya.

Dalilin kawo tiyatar ido a Zamfara

Ya ce an dauki matakin ne domin tallafawa marasa galihu da ke fama da matsalar ido amma ba za su iya biyan kudin aiki ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Wannan shiri ne na gwaji inda marasa lafiya 1000 za su amfana.
“Za a zabi karin wadanda za su ci gajiyar tallafin a kananan hukumomin Anka, Bakura, Bukkuyum, Gummi, Maradun da Talata-Mafara a matakin ba da gudunmawa.
“Wadanda za su ci gajiyar shirin za su kunshi tsofaffi, marasa galihu, mata, da yara.
"Kowane daga cikinsu zai sami damar samun maganin ciwon ido, tiyata, da magunguna yayin atisayen.”

Masarauta ta yabawa Sanata Yari

A nasa jawabin, Sarkin Talata-Mafara, Bello Muhammad-Barmo ya bayyana gudunmawar sanatan a matsayin abin farin ciki, AllNews ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri, Tinubu na da shirin ciyar da kasar nan gaba, shawarin minista ga 'yan Najeriya

Muhammad-Barmo, wanda ya samu wakilcin Galadiman Masarautar Mafara, Alhaji Abubakar Malami, ya bayyana hakan a matsayin kyakkyawan tsarin kare al’umma musamman marasa galihu.

Matsalar ido na daya daga abubuwan da ke damun al’umma a wannan zamanin, musamman duba da yadda kayayyakin fasaha ke kara yawa.

Sabuwar cuta ta bulla a Kano

A wani labarin na daban, a kalla mutane 15 ne suka rasu sakamakon abin da ake zargi cutar diptheria ne a jihar Kano zuwa ranar 18 ga watan Janairu, a cewar Dr Abdullahi Kauran-Mata, masanin cututtuka masu yaduwa.

Ya ce an samu mutum 78 masu dauke da cutar mai gaggawar yaduwa a kananan hukumomi 14 na jihar, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.