An Yanka Ta Tashi: Jerin Jiga-Jigan Siyasa 4 da Suka Karanta Shari’a a Jami’ar Baze
Jami’ar Baze na cikin dambarwa a halin yanzu biyo bayan kwace lasisin koyar da ilimin shari’a da aka yiwa jami’ar.
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
A baya Legit ta rahoto cewa majalisar kula da harkokin ilimin shari’a (CLE) ta dauki matakin ne kwace lasisin na shekaru biyar ne bayan samun jami’ar da laifin saba ka’idojin daukar dalibai 50 a kowane zango kamar yadda majalisar ta amince dashi.
CLE ta kuma ce wuce gona da irin na Jami'ar Baze ya sa ta dauki sama da daliban shari'a 750 tun daga shekarar 2017 a tsangayar shari’a.
An kuma zargi jami’ar da Yusuf Datti Baba-Ahmed ya kafa, da yaye daliban shari’a a cikin shekaru uku tare da basu shaidar digirin LL
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan kuma na aukuwa ne ga daliban da suka shiga jami’ar ta hanyarjarrabawar UTME na hukumar JAMB ba tare da amincewar hukumar NUC, CLE da kuma JAMB kanta ba.
Babban abin da ya fi daukar hankali shi ne, yadda wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasar Najeriya suka halarci jami’ar a shekarun baya kuma suka karanta shari’a.
‘Yan siyasar da suka LL.B a jami’ar Baze
1. Dino Melaye
Sanata Dino Melaye, dan takarar gwamna na jam'iyyar adawa ta PDP a Kogi, 2023 yana daya daga cikin tsofaffin daliban jami'ar Baze.
Tsohon Sanatan na Kogi ta Yamma ya samu digiri na farko a fannin shari’a na LLB a shekarar 2021.
2. Sanata Patrick Ifeanyi Ubah
Sanatan mai wakiltar Anambra ta Kudu kuma tsohon dan takarar gwamna a jam'iyyar YPP, shi ma ya karanci shari'a a jami'ar Baze.
A shekarar 2021 sanata Uba ya tabbatar da cewa ya kammala digiri a hukumance a fannin shari’a (LL.B) daga tsangayar shari’a a wajen taron yaye dalibai da jami’ar ta gudanar a Abuja.
3. Osita Chidoka
Osita Chidoka kwararren dan siyasar Kudu maso Gabas ne daga jihar Anambra. Tsohon shugaban hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) ne, kuma tsohon ministan sufurin jiragen sama.
Ya yi aiki a karkashin hukumar PPD a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Shi ma dai a jami’ar ya kammala karatunsa na digiri a fannin shari’a, kuma ya tabbatar da hakan a shekarun baya.
4. Rotimi Amaechi
A shekarar 2022 ne tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya kammala karatun digiri a Jami’ar Baze a fannin Shari’a.
Amaechi ya ce ya samu gurbin karatun digiri na farko a fannin shari’a a jami’ar mai zaman kanta ne a lokacin da yake rike da mukamin minista.
Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya ce ya hada karatun ilimi da aikin da yake yi a hukumance domin samun nasara.
Meye yasa aka kwace lasisin Baze?
Cibiyar kula da ilimin shari’a (CLE) ta sanya takunkumi na shekaru biyar a tsangayar shari’a da ke Jami’ar Baze da ke birnin Tarayya Abuja.
Cibiyar CLE ta sanya dokar ce bayan zargin wuce gona da iri wurin bayar da gurbin karatu a tsangayar karatun lauya na fiye da mutane 50 a shekara.
Cibiyar ta bayyanna haka ne a cikin wata sanarwa da sakataren rikon kwarya na hukumar, Aderonke Osho ta fitar yayin hira da Channels TV.
Asali: Legit.ng