A Mutunta Shugabanni: Mufti Menk Ya Ba da Shawarin Yadda Najeriya Za Ta Daukaka a Duniya

A Mutunta Shugabanni: Mufti Menk Ya Ba da Shawarin Yadda Najeriya Za Ta Daukaka a Duniya

  • A kwanakin baya ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin babban malamin addini a fadar Aso Rock da ke Abuja
  • Shahararren malamin nan, Mufti Ismail ibn Musa Menk, ya zo Najeriya, inda ya zarce a fadar Tinubu da sauran shugabannin addinin musulunci
  • A ziyarar Mufti, ya jaddada bukatar wanzar da zaman lafiya da jure zama da juna a tsakanin ‘yan Najeriya da ma baki ‘yan waje

FCT, AbujaShahararren malamin addinin Musulunci, Mufti Ismail Musa Menk, ya ziyarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa, Abuja.

Menk da tawagar masana na duniya sun ziyarci Tinubu ne a ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba, inda suka yi kira ga wanzar da zaman lafiya da hadin kai a Najeriya.

Kara karanta wannan

Mufti Menk ya kai ziyara fadar Tinubu, ya ce Najeriya za ta iya zama kasa mafi bunkasa a Afirka

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Menk ya kara jaddada bukatar dukkan ‘yan Najeriya su zauna lafiya da juna tare da mutunta juna duk da bambancin addini da kabila domin ganin nasara a kasar.

Mufti Menk ya ziyarci Najeriya. ya ba da shawari
Shawarin Mufti Menk ga 'yan Najeriya | Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, @muftimenk
Asali: Facebook

Yadda Najeriya za ta ci gaba – daga bakin Menk

A cewarsa, matukar ana son samun daukakar Najeriya, dole ne 'yan kasar su kasance kansu a hade tare da mutunta shugabanninsu, in ji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce shi da tawagar malaman da suka zo sun zo Najeriya ne domin taron wanzar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin ‘yan kasar.

A kalaman malamin dan asalin kasar Zimbabwe:

“Batun shi ne a iya ba ‘yan Najeriya damar zama tare cikin jituwa, a zauna tare; a mutunta juna duk da bambance-bambance da ke tsakani – daga bambancin addinai – domin ganin nasarar wannan al’umma.”

Kara karanta wannan

Yadda faston da ke sayar da tikitin shiga aljanna ya gusar da hankulan yayanmu, ya raba mu

Mufti Menk dai kan zo Najeriya a lokuta da dama don yada karatunsa da kuma ziyartar wurare da yawa.

Mufti Menk ya zillewa 'yar wasan kwaikwayo

A wani labarin, 'yar wasan barkwanci a Najeriya, Maryam Apaokagi wacce aka fi sani da Taaooma, ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta wallafa hotunanta tare da fitaccen malamin Musulunci Mufti Menk.

A kasan wallafar tata, Taaoma ta bayyana tattaunawar da ta yi da Mufti, inda aka ga sun yi hoto suna dariya.

Jama'a a kafar sada zumunta sun yi martani, sun kuma bayyana yadda suke ji game da babban malamin

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.