Gasar Firimiya: Mufti Menk ya ce akwai darasi a nasarar Liverpool

Gasar Firimiya: Mufti Menk ya ce akwai darasi a nasarar Liverpool

A jiya Alhamis, 26 ga watan Yuni, 2020, Jurgen Klopp ya kafa tarihin zama kocin farko da ya kai kungiyar Liverpool ga samun nasara a gasar 'Firimiya' na kasar Ingila.

Liverpool ta shafe shekara da shekaru ba ta samu damar cin gasar kwallon kafa na Ingila ba, tun da aka canza masa salo da suna a cikin watan Fubrairun shekarar 1992.

Mufti Menk wanda shararren malamin addinin musulunci ne a Duniya, ya yi magana game da wannan nasara da Liverpool ta samu bayan ta sha jira na tsawon lokaci.

A cewar Malamin, akwai abin koyi a cikin gwagarmayar da Liverpool ta yi na shekaru 30 kafin Chelsea ta yi wa kungiyar alfarmar doke Man City a Stamford Bridge jiya.

A shafinsa na sada zumunta na Twitter, Shehin ya rubuta: “Ka da ka taba karaya! Ka da ka taba! Bayan shekaru 30! Kungiyar Liverpool (ta lashe gasar) Firimiya.

Never give up! Never! #30YearsLater #Liverpool #PremierLeague - Mufti Menk.

KU KARANTA: 'Dan wasa Oumar Kanoute, ya ginawa wurin sallah a Sifen

Gasar Firimiya: Mufti Menk ya ce akwai darasi a nasarar Liverpool
'Yan wasan Liverpool Hoto: BPL
Asali: Getty Images

Wannan magana ta Mufti Menk ta jawo masa martani daga fiye da mutum 1, 200, Sannan mutane kusan 17, 000 su ka nanata sakon duk daga daren yau zuwa yanzu.

Mutane fiye da 40, 000 ne su ka nuna cewa wannan sako na malamin addinin ya ba su sha’awa.

Wasu sun yi ta sukar malamin, inda su ke ganin cewa ya saki layin koyar da addini, ya shiga harkar kwallon, abin da ake yi wa kallon gafala ko ma haramun.

Wani mutumi mai suna Jabir a shafin Twitter, ya nemi Malamin ya rabu da sha’anin Duniya, ya maida hankali kan addini. Wannan ya jawo shehin ya maida martani.

Da ya ke wanke kansa daga zargi Mufti Menk ya rubuta:

“Kwantar da hankalinka! Idan aka karbi addu’ar mutum bayan shekaru 30 ana roko, farin cikin ya isa ya kauda duk wani bakin ciki na baya, tabbas akwai darasi a gabanmu.”

Ya kara da cewa: “Ka da a karaya! Kuma ban taba daukar bangare ba. Sako ne na addini. Idan zan kara, sai in ce lokacin ka ne da za ka yi addu’a.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel