Babu 'Yancin Yin Haka, Malamin Addini Ya Gargadi Masu Tare Hanya Don Yin Salla, an Yada Bidiyon

Babu 'Yancin Yin Haka, Malamin Addini Ya Gargadi Masu Tare Hanya Don Yin Salla, an Yada Bidiyon

  • Babban malamin addinin Musulunci ya soki mutanen da ke tare hanyoyi saboda yin salla a cikin birane
  • A cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafofin sadarwa, malamin ya gargadi 'yan uwa inda ya ce su tuba daga aikata haka
  • Malamin ya ce ta yaya za ka tare hanyar mutane da yawa da su ke da hakki, idan za a wuce da marar lafiya zuwa asibiti komai na iya faruwa

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kwara - Wani shahararren malamin addinin Musulunci ya yi gargadi mai zafi ga masu tare hanya da sunan yin salla.

A cikin wani faifan bidiyo, an gano malamin na tura sakon gargadi inda ya ke cewa hakan kuskure ne, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

"204k kullun, N6.1m duk wata": Dan Najeriya da ke jinyar wani tsoho ya bayyana abun da yake samu

Malamin addini ya yi huduba mai zafi kan tare hanya yayin da ake salla
Malamin Musulunci ya yi martani kan masu tare hanya idan za su yi salla. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP.
Asali: Getty Images

Wane gargadi malamin ya yi?

Bidiyon wanda wani mai suna @sanusilafiagi ya wallafa a shafin Instagram ya jawo martanin mutane da dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya ce aikata wannan abu babu kyau kuma mummunan dabi'a ce da za ta haddasa rasa rayukan al'umma.

Malamin daga Ilorin ya ce:

"Ya kamata mu kiyaye, mutane su na da 'yanci, kullum ina fadan haka.
"Ba za mu tare hanya ba a matsayin mu na Musulmai da sunan wai muna salla.
"Me yasa za mu tare hanya saboda za mu yi salla, ko da kuwa mintuna biyar ne wani zai iya rasa ransa a cikin mintuna biyar din."

Wane shawari malamin ya bayar?

Ya ce wallahi duk wanda ya ke yin haka ya je ya tuna saboda mummunar dabi'a ce.

Malamin ya kara da cewa:

"Idan aka dauko marar lafiya zuwa asibiti, kai kuma ka tare hanya, ka fada idan ba zai iya mutuwa ba a wannan lokaci."

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sabon rikici ya kaure a wata kasuwar arewa, rayuka 6 sun salwanta

Ya ce akwai wata hauka da ake yi a Ilorin idan mutane za su yi aure ko suna su tare ko wace hanya, wannan hauka ce.

Fasto ya soki mata masu hana mazaje jin dadin aure

A wani labarin, Fasto Mike Bamiloye ya soki matan aure da ke hana mazajensu jin dadin kwanciyar aure.

Mike ya ce irin wadannan mata ba su da mutunci, sun raina mazajensu kuma marowata ne ga mazajensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.