“Babban Yayana Kuma Jagora Mai Mutunci”: Peter Obi Ya Jinjinawa Atiku Yayin da Ya Cika Shekaru 77

“Babban Yayana Kuma Jagora Mai Mutunci”: Peter Obi Ya Jinjinawa Atiku Yayin da Ya Cika Shekaru 77

  • Peter Obi ya taya Atiku Abubakar murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya jinjinawa jagoranci da gudunmawarsa wajen ci gaban Najeriya
  • Obi ya garzaya shafinsa na soshiyal midiya don taya Atikyu murna, yana mai bayyana shi a matsayin "babban yayansa kuma jagora mai mutunci"
  • Obi ya kara jaddada tasirin Atiku wajen karfafa dimokradiyyar Najeriya da bunkasa tattalin arziki da ci gaban ilimi

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Dan takarar jam'iyyar LP a zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi ya garzaya shafinsa na soshiyal midiya don taya Atiku Abubakar murna, yayin da ya cika shekaru 77 a duniya.

Obi ya taya Atiku murnar cika shekaru 77
“Yayana Kuma Jagora Mai Mutunci”: Peter Obi Ya Jinjinawa Atiku Yayin da Ya Cika Shekaru 77 Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Obi ya taya Atiku murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Obi a wasu jerin wallafa da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) ya jinjinawa dan takarar na jam'iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku wanda ya bayyana a matsayin babban yayansa kuma jagora.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da matarsa sun yi bikin cika shekaru 34 da aure

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya taya Atiku godewa Allah kan inda ya kai a siyasar Najeriya, ya rubuta:

"Ya mai girma, babban yayana kuma jagora mai mutunci, Alhaji @atiku Abubakar, Waziri Adamawa, na tayaka murna yayin da kake cika shekaru 77 a duniya a yau.

"Tare da yan uwanka, abokai da tarin masu fatan alkhairi, ina jinjinawa irin gudunmawar da ka bayar wajen ci gaban zamantakewa, siyasa da tattalin arzikin kasarmu mai albarka, musamman ma irin rawar da kake takawa wajen zurfafa dimokradiyyar kasarmu."

Martanin jama'a yayin da Obi ya taya Atiku murna

Wallafar da dan takarar na LP ya yi a dandalin X ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu.

@Obi_BlessedOne ya ce:

"Ya y kyau yallabai Peter Obi. Barka da zagayowar ranar haihuwarka @atiku, na taya ka murna yallabai."

Kara karanta wannan

Wike ya magantu kan yiwuwar karawa da Tinubu a zaben 2027

@jagiriga ya yi martani:

"Barka da zagayowar ranar haihuwa Alhaji Atiku Abubakar.
"Muna fatan zai sadaukar da lokacinsa da karfinsa a yanzu wajen marawa tafiyar obidient baya."

@realOkeyAnya ya ce:

"Idan ka kara wannan "jagorana" a nan gaba, zan toshe ka."

@36Kinniun ya ce:

"Bayan ka lalata masa harkar siyasarsa. "

Atiku ya ziyarci makarantarsa ta firamare

A wani labarin, mun ji a baya cewa dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023, Atiku Abubakar ya ziyarci makarantarsa ta firamare a Jada, jihar Adamawa a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin wallafar da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) inda ya bi sa da hotuna da bidiyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng