“204k Kullun, N6.1m Duk Wata”: Dan Najeriya da ke Jinyar Wani Tsoho Ya Bayyana Abun da Yake Samu
- Wani mai aikin agaji wanda ke kasuwancinsa a Birtaniya ya bayyana makudan kudaden da yake samu a rana bayan ya kula da wani tsoho
- Mutumin ya ce ya samu aikin ne a kwanaki bayan wani dan uwansa ya sanar da shi batun neman mai aiki, kuma bai bata lokaci ba wajen amfani da damar
- A cewarsa, ana biyansa fan 200 a kullun wanda ya kai kimanin N204k kan farashin chanji a yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani dan Najeriya da ke zaune a Birtaniya yana samun albashi N204k duk kwanan duniya a matsayin ma'aikacin agaji.
Mutumin ya wallafa wani bidiyo a TikTok don bayar da labarinsa amma ya ce aikin sam babu sauki saboda yana kula da wani tsoho ne.
A cewar mutumin mai suna Timi, wani dan uwansa ne ya yi masa hanyar samun aikin, kuma bai bata lokaci ba wajen amfani da damar saboda makudan kudaden da ake biya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aikin ya danganci kula da wani tsoho wanda ke da lalurar tabin hankali. Ya ce an dauke shi aiki don ya dunga kai mutumin bandaki da tsaftace masa jiki bayan nan.
Timi ya ce ana biyansa N204k bayan shafe awanni 12 kacal a bakin aikin. Bidiyon da ya wallafa ya nuno shi sanye da rigar leda da sauran kayan kariya.
Da albashin N204k a kullun, Timi zai dunga samun naira miliyan 6.1 a wata idan har ya ci gaba da aikin.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani yayin da matashi ke samun N204k kullun
@Rocket Science ya ce:
"Ina sha'awar yin wannan aiki na tsawon shekaru 10.
@Meera Jay ta ce:
"Wasun su na da boyayyun kamara. Ka yi a hankali."
@Blessing Boluwatife Adeniji ta yi martani:
"Ina fatan ba a su ga wannan bidiyon ba dai."
@Idristeemileyin ya ce:
"Na so wannan dan uwa. Baya kunyar aikin da yake yi."
@princessdammy__ ta ce:
"A nan Amurka kurkuku za ka je kai tsaye saboda daukar wannan bidiyon kadai."
Matashi ya koka da tsadar rayuwa
A wani labarin, mun jin cewa Najeriya na fuskantar matsananciyar matsala ta tattalin arziki, inda tsadar farashin kayayyaki ya kai kololuwa a tarihinta a 2023.
Tsadar rayuwa dai ta yi sanadiyyar durkusar da karfin siyayyar yan Najeriya da dama musamman matasa da masu karbar albashi.
Asali: Legit.ng