Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Garuruwa 4 a Arewa, Sun Tafka Ɓarna Tare a Sace Mutum 150
- Yan bindiga sun kara kai kazamin hari kauyuka huɗu a yankin ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara ranar Jumu'a
- Mazauna garin sun ce maharan sun shiga kauyukan lokaci ɗaya, suka kashe mutum ɗaya kana suka tafi da wasu 150
- Wani mutumi ya bayyana cewa a yanzu ba su da kowa sai Allah domin ba abinda jami'an tsaro suke yi na kai masu ɗauki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Wasu miyagun ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 150 yawancinsu mata da yara a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a ranar Juma’a.
A cewar mazauna garin, yan bindigan sun kuma kashe mutum ɗaya a harin wanda ya shafe sama da awa ɗaya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wannan sabon hari na zuwa ne mako ɗaya bayan ƴan fashin daji sun sace mutane 17 a kauyen Ruwan Ɗorawa da ke wannan ƙaramar hukuma ta Maru a Zamfara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda maharan suka kai sabon hari ƙauyuka 4
An tattaro cewa a sabon harin, yan bindiga sun shiga ƙauyuka huɗu, Mutunji, Kwanar-Dutse, Sabon-Garin Mahuta da Unguwar Kawo a yankin Maru.
Wani mazaunin ƙauyen Mutunji, daya daga cikin kauyukan da aka kai harin, ya ce ‘yan bindigan sun shiga kauyukan da misalin karfe 9 na daren Juma’a lokaci ɗaya.
Mutumin ya ce:
"Sun shiga kauyen Mutunji, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi domin tsorata mutane, nan da nan mutane suka fara gudu. Maharan sun kama masu rauni mafi akasari mata da yara, saura suka gudu."
"Na yi kokarin kiran abokina a kauyen Kwanar-Dutse domin neman agaji amma ya faɗa mun cewa su ma an kai musu hari, ya faɗa mun a lokacin yana ciki daji ya ɓuya da wasu mutane."
Wani mazaunin garin, wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa, ya ce watakila ’yan bindigar tare suke amma suka raba kansu gida hudu, kowane kashi ya shiga ƙauye ɗaya.
“Mun samu labarin cewa bayan farmakan kauyukan hudu, ‘yan bindigar sun sake haduwa suka kwashe wadanda suka ɗauko zuwa cikin daji."
"A yanzu yan bindiga na cin karensu babu babbaka, ba wanda ke tanka musu daga jami'an tsaro, wani lokacin muna samun labarin sun taho amma ko mun gaya wa hukumomi ba zasu yi komai ba."
Dakarun Sojoji Sun Halaka Yan Bindiga a Zamfara
A wani rahoton kuma Yan bindiga sun mutu yayin da sojoji suka kai farmaki kan sansanin yan ta'adda a kauyuka da dama a jihar Zamfara
Mai magana da yawun rundunar Operation Hadarin Daji, Kaftin Yahaya Ibrahim ya ce sojoji sun raba yan bindiga hudu da duniya
Asali: Legit.ng