Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Manyan Nade-Nade Masu Muhimmanci Guda 8

Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Manyan Nade-Nade Masu Muhimmanci Guda 8

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da nadin sabbin sakatarorin din-din-din a ranar Juma’a, 24 ga watan Nuwamba
  • Hadimin shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya ce sabbin sakatarorin din-din-din guda takwas da aka nada suna cikin ma’aikatar gwamnatin tarayya
  • Ngelale ya bayyana cewa nadin nasu na zuwa ne bayyana ofishin shugaban ma'aikatan tarayya ya kammala tsarin zaben

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Fadar shugaban kasa, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabbin sakatarorin din-din-din guda takwas a ma'aikatar tarayya.

Tinubu ya amince da nadin ne bayan kammala tsarin zabo mutanen da ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya ya yi.

Tinubu ya nada sakatarorin dindindin
Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Manyan Nade-Nade Masu Muhimmanci Guda 8 Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Mai ba shugaban kasar shawara ta musamman kan harkokin labarai, Cif Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga tsakani yayin da yan majalisa suka fara shirin tsige gwamnan APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fredrick Nwabufo, Babban mai ba shugaban kasa shawara kan hulda da jama'a, ya wallafa labarin a shafinsa na dandalin X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @FredrickNwabufo.

Jerin sunayen sabbin sakatarorin din-din-din da aka nada

  • Ndakayo-Aishetu Gogo
  • Adeoye Adeleye Ayodeji
  • Rimi Nura Abba
  • Bako Deborah Odoh
  • Omachi Raymond Omenka
  • Ahmed Dunoma Umar
  • Watti Tinuke
  • Ella Nicholas Agbo

Tinubu ya yi hasashen cewa sabbin sakatarorin za su yi amfani da kwarewarsu da cancantarsu wajen aiwatar da ajandarsa na sabonta fata.

"Shugaban kasa Tinubu ya yi hasashen cewa sabbin sakatarorin na din-din-din, kasancewarsu zakaran gwajin dafi cikin wadanda suka cancanta bayan tantance su, za su yi amfani da kwarewa da cancantarsu wajen aiwatar da manufar sabonta fata don farfado da ayyuka a daukacin ma’aikatun tarayya saboda ra'ayin mutanen Najeriya."

Kara karanta wannan

Ku bar ganin Ganduje haka; raina kama ne kaga gayya - Jigo a PDP ya ankarar da Kwankwaso

Wike ya magantu kan zaben 2027

A wani labarin, mun ji cewa Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya ce shi dan amana ne kuma ba zai kara da Shugaban kasa Bola Tinubu ba a zaben 20217.

Wike ya bayyana hakan ne yayin wata hirar kafar watsa labarai a ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba, wanda Legit Hausa ta bibiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng