Gwmnatin Ganduje Ta Dauki Daliban JSS Dan Shekaru 13 Aikin Gwamnati a Kano, SSG Na Kano
- A wani abu mai kamar al'amara, gwamnatin jihar Kano ta gano wasu daliban makarantar sakandire (JSS da SSS) a cikin ma'aikatan jihar
- Haka zalika, gwamnatin ta gano dubunnan ma'aikatan da ta ce gwamnatin Abdullahi Ganduje ta dauka aiki ba bisa ka'ida ba, ciki har da 'yan kasa da shekara 18
- Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin Abba Kabir ta kafa wani kwamiti da zai binciki dukkanin wadanda gwamnatin Ganduje ta dauka aiki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta fallasa wata badakala da ta ce gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi na daukar ma'aikata, inda ta gano yara 'yan sakandire a masu daukar albashi.
Akwai dubunnan mutane da gwamnatin Abba Kabir ke ganin gwamnatin baya ta dauka aiki ba bisa ka'ida ba, da wannan ta dakatar da albashin su.
Haka zalika, an kafa wani kwamiti da zai tantance duk wasu ma'aikata da gwamnatin Ganduje ta dauka aiki a jihar don gano wadanda basu cancanta ba, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sama da ma'aikata dubu uku aka dauka ba bisa ka'ida ba - SSG, Kano
Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa kwamitin ya ba da shawarar korar wadanda ba su cancanta ba, wadanda suka haura dubu uku.
A cewarsa:
"Da yawa daga wadanda aka dauka aikin babu sunayensu a cikin kasafin da aka amince da shi na 2023 kuma ba su nuna sha'awar yin aikin a rubuce ba.
Yawancin wadanda aka dauka aikin ba su bi matakan tantancewa kamar yadda dokokin aikin gwamnati ya tanadar ba.
An gano wadanda aka dauka aikin suna amfani da takardun bogi, wasu kuma ba 'yan asalin jihar ba ne alhalin akwai dimbin ’yan asalin da ba su da aikin yi kuma sun cancanta.
An samu daliban sakandire a masu daukar albashi - SSG, Kano
Sakataren gwamnatin ya kuma ce:
"Mun gano wasu ma dalibai ne da ke kan yin karatu ciki har da 'yan sakandire (JSS) da (SSS), wasu kuma sun farkon karatun jami'a, wasu kuma suna bautar kasa (NYSC)."
"Akwai wadanda su ko shekarun balaga ba su kai ba, kuma a haka ake biyan wadannan albashi duk wata, matsayin ma'aikatan gwamnatin jiha."
Magoya bayan NNPP sun yi addu'o'i don nasarar Gwamna Abba na Kano
A wani labarin, an samu tashin hankali a Kano, yayin da magoya bayan jam'iyyar NNPP suka yi gangamin salloli da addu'o'i duk da gargadin 'yan sanda, Legit Hausa ta ruwaito.
A yayin da ake wannan hargitsin, wani dan jam'iyyar ya ce dole su gudanar da addu'a da zanga-zangar lumana kan rashin adalcin da ya ce an yi masu
Asali: Legit.ng