Gwamnatin Birtaniya Ta Bude Kofa Ga Daliban Najeriya Don Neman Tallafin Karatu a Jami’o’i 17
- Daliban Najeriya na da damar neman tallafin Euro 10,00 daga gidauniyar GREAT don yin karatun PGD a jami'o'in kasar Burtaniya a zangon karatu na 2024-25
- Wannan tallafin hadin guiwa ne tsakanin gidauniyar GREAT Britain da kuma hukumar kasar Birtaniya, da suka shafi jami'o'in Ingila, Wales, Scotland da Ireland ta Arewa
- Dole sai kai dan asalin Najeriya ne, da ke da sakamakon karatun digiri na farko, kuma ka cika ka'idar jin yaren turanci, da sauransu kafin ka samu tallafin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kasar Birtaniya - Dalibai daga Najeriya da wasu kasashe 14 sun samu damar neman tallafin karatu daga gidauniyar GREAT gabanin zangon karatu na shekarar 2024-25.
Tallafin zai ba daliban Najeriya da sauran kasashen damar samun Euro 10,000 don biyan kudin makaranta a shirye-shiryen karatu na matakin PGD a jami'o'in Birtaniya.
Legit Hausa ta tattaro cewa tallafin hadin guiwa ne tsakanin gidauniyar GREAT Britain da kuma hukumar kasar Birtaniya da suka shafi manyan jami'o'in kasar Birtaniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai guraben karatu 210 da jami'o'i 71 ke bayarwa a duk faɗin Ingila, Wales, Scotland da Ireland ta Arewa.
Gidauniyar karatu ta GREAT: Jerin kasashe da za su amfana
- Bangladesh
- China
- Egypt
- Ghana
- Greece
- Kenya
- India
- Indonesia
- Malaysia
- Mexico
- Nigeria
- Pakistan
- Thailand
- Turkey
- Vietnam
Gidauniyar karatu ta GREAT: Jami’o’in da ‘yan Nijeriya ke iya shiga
A zangon karatu na 2024-25, daliban Najeriya na iya neman tallafin karatun digirin PGD daga gidauniyar GREAT a jami'o'in da za mu lissafa kasa.
Ana shawartar dalibai masu sha'awar tallafin da su ziyarci shafukan jami'o'in da za a jero kasa don ganin kwasa-kwasan da dalibi zai iya nema da kuma bayanin yadda ake cike wa.
- Jami'ar City ta Landan
- Jami'ar Edge Hill
- Jami'ar Keele
- Jami'ar Nottingham Trent
- Jami'ar Oxford Brookes
- Kwalejin kirkire-kirkire ta The Royal
- Jami'ar Sheffield Hallam
- Jami'ar Manchester
- Jami'ar kwalejin Landan
- Jami'ar Birmingham
- Jami'ar Bristol
- Jami'ar Derby
- Jami'ar Anglia ta Gabas
- Jami'ar Glasgow
- Jami'ar Southampton
- Jami'ar Warwick
- Jami'ar York
Gidauniyar karatu ta GREAT: Abubuwan da ake bukata daga dalibai
- Zama cikakken dan Najeriya
- Mallakar digiri na farko
- Samun shaidar iya harshen Ingilishi na UK HEI
- Ka kasance kana halartar tarukan manyan daliban gidauniyar GREAT mazauna Birtaniya
- Ka kasance kana tuntunbar hukumar Birtani da HEI da zama jakadan gidauniyar GREAT na -gari
- A matsayin tsohon dalibi na gidauniyar GREAT, ka rinka tattauna wa da masu sha'awar neman tallafin game da rayuwarka a Birtaniya
Gidauniyar karatu ta GREAT: Yadda za a nemi tallafin karatun
- Ziyarci shafukan jami'o'in da aka lissafa sunayensu
- A nemi tallafin karatun na mutum daya ta bin umarnin da aka bayar a shafukan yanar gizon kowace jami'a
- Wa'adin neman tallafin karatu daga gidauniyar GREAT ya bambanta bisa ga kowace jami'a. Don cikakkun bayanai kan wa'adin, a duba shafukan jami'o'in.
- Jami'o'in za su sanar da sunayen daliban da suka samu nasara kai tsaye ga daliban.7
- Kowacce jami'a za ta ba daliban da suka yi nasara tallafin karatun bayan sun kammala rijista.
Yadda ’Yan Najeriya Za Su Iya Yin Karatu Kyauta a Kasar Faransa
A wani labarin, ofishin Jakadancin Faransa a Najeriya, ya sanar da bayar da cikakken tallafin karatu ga daliban kasar don ci gaba da karatun digiri, Legit Hausa ta ruwaito.
Wannan damar ta hada da tallafin sufuri, alawus-alawus na wata-wata, shawarwari kan gidajen zama, kula da lafiya, kudaden biza, da kuma kudaden karatun kasar
Asali: Legit.ng