Gwamna Dauda Lawal Ya Kashe N400m Kan Balaguro Zuwa Kasashen Waje? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamna Dauda Lawal Ya Kashe N400m Kan Balaguro Zuwa Kasashen Waje? Gaskiya Ta Bayyana

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta musanta rahotannin da ake yaɗa wa cewa Gwamna Dauda Lawal ya kashe N400m wajen balaguro zuwa ƙasashen waje
  • Gwamnatin a cikin wata sanarwa da ta fitar ta bayyana cewa rahotannin an ƙirƙire su ne domin kawo ruɗani
  • Sanarwar ta yi nuni da cewa tun bayan hawan gwamnan kan karagar mulki, sau uku kawai ya yi tafiya zuwa ƙasashen waje

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya musanta zargin da ake yi masa na amfani da sama da Naira miliyan 400 wajen tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, an tattaro cewa wani labari da aka buga ta yanar gizo ya yi iƙirarin cewa gwamna Dauda Lawal ya kashe N170,276,294.31 kan tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje, N221,567,094 kan tafiye-tafiyen cikin gida, da kuma N6,929,500.00 kan tsaronsa cikin wata uku.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC mara lafiya ya kashe N7.3bn lokacin jinya? APC ta bayyana gaskiya

Gwamnatin Zamfara ta musanta kashe N400m
Gwamna Dauda Lawal ya musanta kashe N400m kan balaguro zuwa kasashen waje Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Da yake mayar da martani, mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, ya ce da gangan ne masu son tada rigima suka ƙirƙiri labarin da nufin karkatar da hankali daga gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

“Mun karanta wani rahoto da ke cewa Gwamna Dauda Lawal ya kashe sama da Naira miliyan 400 wajen tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje. Wannan ƙarya ce da nufin ɓatan sunan gwamnan."
"Yin gaskiya da riƙon amana sune ginshiƙin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal. Ana iya samun dukkanin bayanan da suka dace a gidan yanar gizon gwamnatin jihar Zamfara a zamfara.gov.ng."
"An sanya a shafin yanar gizon cikakken rahoto kan yadda ake gudanar da kasafin kuɗi, wanda ke ba da cikakken bayanin yadda Gwamna ke kashe kuɗaɗe a tafiye-tafiye da sauran ayyuka."

Kara karanta wannan

Matawalle vs Lawal: Gwamnan PDP ya faɗi wanda zai samu nasara a zaben da za a ƙarisa a Zamfara

"A ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal, mun aiwatar da tsarin gaskiya da riƙon amana, ba tare da barin ƙofar yin amfani da kuɗade ta hanyar da ba ta dace ba”.

Tafiye-tafiyen Gwamna Lawal

Idris ya fayyace cewa, wannan bahasin ya samo asali ne daga kuskuren fassara bayanan kasafin kuɗin da aka yi da gangan, inda ya jaddada cewa, rukuni na ɗaya da na biyu da na uku suna ƙarƙashin gwamnatin da ta shuɗe ne.

Sanarwar ta ce:

"Domin haka yana da muhimmanci a fayyace cewa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi balaguro zuwa ƙasashen waje sau uku ne kacal tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023."
"Tafiyen kasashen waje guda uku sune: halartar taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) a ƙasar Amurka, wani taron bita na United Nations Development Programme (UNDP) a birnin Kigali, Rwanda, da kuma ganawa da shugaban bankin raya nahiyar Afirika Dr Akinwumi A. Adesina a birnin Abidjan na ƙasar Cote d'Ivoire."

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Atiku Abubakar ya maida martani mai zafi kan tsige gwamnonin arewa biyu

Ayyukan Ofis Sun Lashe N6bn a Osun

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya kashe N6bn wajen gudanar da ayyukan ofis cikin wata uku.

Gwamnan ya kuma lashe N2bn wajen siyan kayan abinci da kayan sha da jindaɗin ma'aikata a cikin wata uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel