“Na Rigada Na Siya Katifu da Gadaje”: Shahararren Dan Majalisa Aai Aurar da Yan Mata 100
- Wani dan majalisar tarayya, Sani Yakubu Noma, ya bayyana aniyarsa na aurar da yan mata marayu 100 a jihar Kebbi
- Dan majalisar ya bayyana cewa shirin auren na daya daga cikin gudunmawar da yake bayarwa wajenkula jin dadin marayu a mazabar sa
- Noma ya ce za a daura auren ne a fadar mai martaba Sarkin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera a ranar Asabar 25 ga watan Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Wani dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Argungu/Augie ta jihar Kebbi a majalisar wakilai, Sani Yakubu Noma, ya ce ya kammala duk wasu shirye-shirye don aurar da yan mata marayu su 100.
Da yake magana da manema labarai a mahaifarsa ta Argungu da ke jihar Kebbi, dan majalisar ya ce shirin yi wa yan matan auren gata yana daga cikin gudunmawarsa na kula da jin dadin marayu a mazabarsa.
Za a daura auren yan mata 100 a fadar Sarkin Argungu
Ya ce za a yi taron daurin auren ne a fadar sarkin Argungu, Mai martaba Alhaji Sama’ila Muhammad Mera a ranar Asabar, jaridar Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Post ta nakalto Yakubu Noma yana cewa:
"An kafa wani kwamiti domin ganin aiwatar da taron cikin nasara. Wadanda aka zaba za a yi wa auren gatan an zabo su ne daga kananan hukumomi biyu da nake wakilta a majalisar dokokin tarayya.
"Tuni na rigada na siyawawadanda suka ci gajiyar shirin kayan gadaje, katifu, kayan daki masu muhimmanci da sauran abubuwan bukata a gidan aure."
Dan majalisa ya aurar da marayu
A wani labari makamancin wannan, Legit Hausa ta kawo a baya cewa dan majalisa mai wakiltan mazabar Gusau/Tsafe a majalisar wakilai ta kasa, Kabiru Ahmadu Maipalace, ya dauki nauyin auren wasu yan mata marayu tara, karkashin shirinsa na kula da jin dadin mata, marayu da marasa gata.
Da yake gabatar da kayan daki da sauransu ga amaren a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, Maipalace ya ce ya yi hakan ne don cika alkawarin zabe da ya daukarwa al'umma.
Maipalace wanda ya samu wakilcin sakatarensa, Mustafa Hassan a wajen taron, ya bayyana cewa wannan abu da ya yi yana daga cikin shirinsa na tallafawa marasa gata karkashin kwamitinsa kan mata, marayu da marasa gata.
Asali: Legit.ng