An Nada Sabon Shugaba a Bankin Musulunci Na Ja’iz, an Bayyana Sunanshi
- Kwamitin gudanarwa na bankin Ja’iz ya amince da nadin sabon shugaban bankin bayan sahalewar bankin CBN
- Sabon shugaban mai suna Haruna Musa ya shafe shekaru 27 ya na aiki a bangaren banki wanda ya ba shi damar darewa kujerar
- Nadin Haruna Musa zai fara aiki nan take bayan sahalewar Babban Bankin Najeriya, CBN a ranar 21 ga watan Nuwamban 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Bankin Musulunci a Najeriya, Ja’iz ya amince da nadin Haruna Musa a matsayin sabon shugaban bankin.
Kwamitin gudanarwa na bankin ne ya amince da nadin Musa wanda kwararren ma’aikacin banki ne da ya shafe shekaru a bangaren aikin banki.
Yaushe aka nadin zai fara aiki?
Nadin Musa zai fara aiki nan take bayan sahalewar Babban Bankin Najeriya, CBN a ranar 21 ga watan Nuwamban 2023, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai, Mohammed Baba Kandi ya fitar inda ya ce sabon shugaban ya shafe shekaru 27 a bangaren aikin banki.
Kandi ya ce Musa ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria da Jami’ar Bayero da ke jihar Kano da kuma Jami’ar Cranfield da ke Ingila.
Ya ce a yanzu haka ya na kan karatunsa da digirin digirgir a Jami’ar Bankin Musulunci da Harkokin Kudade da ke Malaysia.
Waye ne sabon shugaban bankin Ja’iz?
Sanarwar ta ce:
“A Jami’ar Cranfield, Haruna ya samu shaidar kammala digiri na biyu daga shekarar 2008 zuwa 2009.
“Ya kuma samu wani digiri din na biyu a bangaren kasuwanci a Jami’ar Bayero da ke Kano daga shekarar 1997 zuwa 1998.
“Yayin da ya samu shaidar kammala digiri a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria daga shekarar 1987 zuwa 1991.”
Kafin nadin Musa a matsayin shugaban bankin, shi ne babban darakta a bankin Guarantee Trust inda ya shafe shekaru takwas, cewar Leadership News.
Babu ranar barin amfani da tsaffin kudade, CBN
A wani labarin, Babban Bankin Najeriya, CBN ya umarci ‘yan Najeriya da su ci gaba da amfani da tsaffin kudade.
Bankin ya ce babu ranar barin amfani da tsaffin kudaden inda ya ce dukkan kudaden halastattu ne.
Asali: Legit.ng