Matatar Man Najeriya Ya Fara Aiki, Ya Tace Lita Miliyan 600 Na Fetur, Ya Shirya Goggaya
- Matatar mai ta zamani mallakar Waltersmith Petroman Oil Limited ta samu yabo daga gwamnatin tarayya
- Matatar man da ke jihar Imo, ta taimaka wajen samar da mafita ga kalubalen makamashi da Najeriya ta dade ta na fama da shi
- Tuni dai matatar ta ke samar da sama da lita miliyan 600 na kayayyaki iri daban-daban tare da yi wa manyan motoci 20 lodi a kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Imo - Heineken Lokpobiri, karamin ministan albarkatun man fetur, ya yabawa matatar mai ta WalterSmith Modular bisa cimma muradun kasar kan samar da makamashi.
Matatar man wacce ta ke a Ibigwe, karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar Imo tana samar da lita miliyan 600 na kayayyaki iri daban-daban.
A wani rangadi a matatar, Lokpobiri ya bayyana jin dadinsa da yadda ayyukan matatar mai ta WalterSmith ke gudana, Legit ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya da matsalolin makamashi
Ministan ya kuma bayyana cewa matatun mai na zamani su ne hanya mafi saurin magance matsalolin makamashin Najeriya, in ji rahoton Vanguard.
Kalamansa:
"A matsayina na karamin minista, alhakina ne na tabbatar da cewa an samu isassun albarkatun man fetur har zuwa lokacin da za a dawo da ayyukan tace matatun mai mallakin gwamnatin kasar nan."
"Ina farin cikin kasancewa a nan don ganin abin da ke faruwa kuma in karfafa guiwar WalterSmith; Tabbas akwai yiwuwar mu iya magance matsalolin makamashinmu a kasar nan."
Karfin matatar man
Matatar mai ta WalterSmith na samar da sama da lita miliyan 600 na kayayyaki daban-daban daga wannan matatar tare da yi wa manyan motoci 20 lodi a kullum
Babban sakataren ma'aikatar "Content Development and Monitoring Board (NCDMB) ta kasa, Simbi Wabote, ya bayyana cewa, gwamnati za ta tallafawa matatar mai ta WalterSmith.
“Gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa masu matatun mai na zamani ko da kuwa ba kudi ba za mu bayar ba, don haka za mu yi duk abin da za mu iya don tallafa wa WalterSmith."
- Simbi Wabote
Da gaske matatar man Dangote za ta kawo tsadar mai a 2024?
A wani labarin, rahoton EIU ya sanar da cewa fara aiki a matatar Dangote zai iya kara tashin farashin man fetur a kasar a shekarar 2024, Legit Hausa ta rawaito.
Rahoton ya kuma ce babban matatar wanda ta kai girman 650,000 zai kawo karshen shigo da mai na NNPC da sauran ‘yan kasuwa.
Asali: Legit.ng