Za’a gina sabon matatar mai a Katsina, zai ci $2 billion

Za’a gina sabon matatar mai a Katsina, zai ci $2 billion

Hadin kan kasar Nijar da Najeriya ya kawo amfanin gina sabuwar matatar man fetur a karamar hukumar Mashi, a jihar Katsina. Lissafin masu sanya hannun jari ya nuna cewa zai ci $2biliyan.

Wannan matatar mai da ake shirin ginawa na da karfin tace gangan mai 150,000 a ranan daya idan aka kammala a shekarar 2021.

Karamin ministan man Najeriya, Dr Ibe Kachikwu,da ministan man kasar Nijar, Foumakaye Gado, a ranar Talata sun rattaba hannu kan takardan yarjejeniya a fadar shugaban kasa da ke Aso Villa Abuja.

KU KARANTA: Wani Fasto ya ga ta kansa, Sojojin ruwa sun kaiwa matatar mansa sumame

Kachikwu yace: “ A yanzu, mun shirya zukatanmu kan karasawa cikin shekara uku amma ya danganta da yadda abubuwa suka kasance.

Game da cewar ministan, akwai yiwuwan a sake kara girman matatar man fetur da ke jihar Kaduna.

“Za’a gina a Katsina amma za’a iya karasawa da shi Kaduna. Ku sani cewa tunanin gina matatar man ya fara ne lokacin da kasar Nijar tayi niyyar jan layin dogo daga Nijar zuwaKaduna.”

“Dalilin da yasa aka fasa yin hakan shine kyan danyen man feturin Najeriya ya fi na Nijar saboda sai mun dauki kashi 90 na man Najeriya da kasha 10 na Nijar kuma hakan bai yi ba.”

A taron kaddamarwa, wani mai sanya hannun jari, Alhaji Ibrahim Zakari, y ace kudi dala biliyan biyu ake bukata na gina matatar man.

Ya yi alkawarin bayar da kudi kasha 100 na farko domin kaddamar da aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng