Mutane Sun Kama Lahaula Sakamakon Shirin Rusa Gidaje 677 Da Gwamnati Za Ta Yi
- Hukumar gidaje ta tarayya tayi shiri tsaf domin a ruguza gine-gine fiye da 600 da aka yi a Amuwo-Odofin a Legas
- Jami’an FHA sun tabbatar da cewa mutane sun rika yin gini a kan tituna da hanyoyin ruwa ba tare da umarni ba
- Akwai gidaje sama da 700 da rushe-rushen zai shafa, ana sa ran hukuma ba za ta ruguza su daga sama har kasa ba
Lagos - Hukumar gidaje ta tarayya (FHA) ta shaida cewa ta shirya ruguza gidaje 677 a sakamakon sabawa doka da aka yi wajen gina su.
Bayan wadannan gidaje da za a rusa har kasa, hukumar ta FHA za ta yi wasu ‘yan rushe-rushe da za su shafi wasu gidaje akalla 744.
Kamar yadda The Guardian ta kawo rahoto, za a ayi wannan aikin rusau ne a unguwar FESTAC a yankin Amuwo-Odofin a Legas.
Shugaban FHA na shiyyar Kudu maso yamma, Akintola Olagbemiro ya yi wannan bayani lokacin da ya ziyarci unguwar da za ayi aikin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Akintola Olagbemiro ya je Amuwo-Odofin domin ganin yadda mutane su ka yi watsi da tsarin hukuma wajen gina gidajen na su.
An yi gine-ginen gidaje babu umarni
Jami’in yake cewa duk da wasiku da ziyarar da aka rika kai wa masu ruwa da tsaki, mutane sun cigaba da aikin gine-gine babu ka’ida.
Daily Post ta ce an zargi masu gidajen da yin gini a kan ruwa ba tare da bin dokoki ba.
A cewar Olagbemiro, jama’a sun rika shiga cikin filayen Festac ba tare da ka’ida ba, sun yi gine-gine barkatai a wuraren da bai dace ba.
Shirin da hukumar FHA ta ke yi
Jami’in ya kara da FHA na kokarin ganin sun gano yadda za a magance matsalar shiga filin gwamnati domin a rayu cikin natsuwa.
Jerin manyan motocin karau da ake zargin tsohon Gwamnan CBN Emefiele ya siya da N1.2bn na kudin kasa
Mataimakiyar Manajar FHA ta Kudu maso yamma, Francisca Michael-James ta ce za su bukaci jami’an tsaro domin fara rusa gine-gine.
Francisca Michael-James take cewa akwai ginin da aka yi a kan tituna da hanyoyin ruwa.
Abin da za a fara yi shi ne a rusa bangaren gine-ginen domin a fitar da hanya, hakan zai shafi gidaje 1, 421 da za a ruguza ko za a taba.
Za a gyara gidaje a Aso Rock
Watanni 5 da hawa mulki, sai ga labari cewa Shugaban Najeriya zai batar da kusan N10bn a kan gyaran gidajen da su ke kwana a ciki.
Sannan za a gyara wani gidan shugaban kasa da ke Legas duk da fadar shugaban kasa ta koma Abuja shekaru fiye da 30 da suka wuce.
Asali: Legit.ng