Ma'aikatan FG Dubu 5 Ne Za Su Rasa Albashin Watan Disamba Kan Dalili 1 Tak, Wasu Sun Samu Shiga
- Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya akalla dubu 5 ne za su rasa albashinsu na watan Disamba saboda wasu matsaloli a takardunsu
- Shugaban kungiyar manyan ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Tommy Okon shi ya bayyana haka a jiya Talata 21 ga watan Nuwamba
- Okon ya ce sun yi nasarar mayar da ma'aikata dubu biyu da dari bakwai kan tsarin biyan albashi
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kungiyar manyan ma'aikata a Najeriya, Tommy Okon ya ce akalla ma'aikata dubu 5 za su rasa albashin watan Disamba.
Ya ce ma'akatan za su samu matsalar saboda rashin daidaito a takardar daukarsu aiki da kuma ranar haihuwarsu, Legit ta tattaro.
Mene dalilin matsalar a albashin ma'aikatan?
Okon ya ce kungiyar ta hada kai da shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya don tura sunayen su tare da tabbatarwa, cewar News Direct.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da ya ke bayyana ci gaban da aka samu, Okon ya ce ma'aikata kusan dubu 3 ne aka mayar da su kan albashi bayan tantance su.
Ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi gaggawar daukar mataki don dakile matsalar rashin biyan albashin watan Disamba a kan lokaci.
Yayin da ya ke ganawa da manema labarai, Okon ya ce sun kammala tantance ma'aikata dubu 17 da aka cire sunayensu a tsarin biyan albashi.
Mene Okon ke cewa kan ma'aikatan?
Punch ta tattaro Okon ya na cewa:
"Zuwa yanzu, wadanda su ka samu dama aka tantance su ne kawai da aka yi kuskuren cire sunayensu za su samu albashi.
"Yayin da ma'aikata dubu 5 har yanzu su na da matsala a ranar haihuwarsu da ke jikin takardar daukarsu aiki.
"Fiye da ma'aikata dubu 3 an mayar da sunayensu, yayin da mutum dubu 5 an mika sunayensu don shawo kan matsalar."
Kotu za ta yi hukunci kan amfani da tsaffin kudade
A wani labarin, kotun koli ta sanya 30 ga watan Nuwamba a matsayin ranar yanke hukuncin amfani da tsaffin kudade.
Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta bukaci kotun ta sake duba wa'adin karbar kudaden.
Asali: Legit.ng