Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Gona, Sun Yi Awon Gaba da Matan Aure 8
- Wasu matan aure sun faɗa hannun ƴan bindiga lokacin da su ke tsaka da gudanar da aikin gona a Abuja
- Miyagun ƴan bindigan sun yi awon gaba da matan su takwas a ƙauyen Gwombe cikin ƙaramar hukumar Kuje
- Sace matan auren na zuwa ne bayan ƴan bindiga sun yi awon gaba da mahaifin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Kwali a Abuja
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƴan bindiga sun yi awon gaba da matan aure takwas a wata gona da ke ƙauyen Gwombe a masarautar Gwargwada cikin ƙaramar hukumar Kuje a birnin tarayya Abuja.
Sace matan dai na zuwa ne kimanin sa'o'i 48 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da mahaifin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Kwali, tare da wasu mutum shida a ƙauyen Yewuti.
Wani mazaunin Gwargwada mai suna Usman Yakubu ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce matan suna girbin iri na benni ne a lokacin da ƴan bindigar ɗauke da bindigu ƙirar AK-47 suka kewaye su.
An tabbatar da aukuwar harin
Wani basarake daga wani ƙauye a masarautar, wanda ya gwammace a sakaya sunansa, ya tabbatar da sace mutanen, yana mai cewa:
“Haƙiƙa, huɗu daga cikin matan ƴan gida daya ne."
Ya ƙara da cewa:
"Ina zargin waɗannan ƴan bindiga da suka yi garkuwa da matanmu na daga cikin waɗanda suka tsere daga ƙauyen Kabbi da ke makwabtaka da su da ke yawo a cikin daji bayan da ƴan sakai na Miyetti Allah suka kashe wasu daga cikinsu a ƙarshen mako."
Babu wani martani daga kakakin rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Adeh Josephine, kan lamarin.
Ƴan Bindiga Sun Sace Matar Dagaci
A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Ruwandorawa cikin ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Ƴan bindigan a yayin harin sun halaka ɗan sanda ɗaya tare da yin awon gaba da matar dagacin ƙauyen da wasu mutum 15
Asali: Legit.ng