"Kada Ka Yi Barci": Gabanin Hukuncin Kotu, Babban Malamin Addini Ya Gargadi Dan Takarar Gwamnan PDP

"Kada Ka Yi Barci": Gabanin Hukuncin Kotu, Babban Malamin Addini Ya Gargadi Dan Takarar Gwamnan PDP

  • Primate Elijah Ayodele ya buƙaci David Emmanuel Ombugadu, ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa a zaɓen 2023 da ya yi taka tsan-tsan
  • A kwanakin baya ne kotun zaɓe ta tsige Gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC tare da bayyana Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar
  • Sai dai, Gwamna Abdullahi Sule ya ɗaukaka ƙarar soke zaɓensa da kotun zaɓe ta yi a kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Lafia, jihar Nasarawa - Primate Babatunde Elijah Ayodele ya buƙaci David Ombugadu, ɗan takarar jam'iyyar PDP a jihar Nasarawa, da ya sa ido sosai yayin da kotun ɗaukaka ƙara za ta yanke hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Kano: An fada wa Kotun Koli wanda za ta ayyana ya yi nasara a tsakanin Gwamna Abba da Nasiru Gawuna

Ayodele ya buƙaci ɗan takarar na jam'iyyar PDP da kada ya yi wasa a ƙoƙarin da ya ke yayin da ake jiran hukuncin da kotun ɗaukaka ƙarar za ta yanke.

An shawarci David Ombugadu na PDP
Kotun daukaka kara ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Nasarawa Hoto: D. Ombugadu, Abdullahi Sule
Asali: Facebook

Malamin addinin ya buƙaci mai fatan zama gwamnan da ya koma ga Allah don samun nasara da tagomashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasarawa: “Dole ne ɗan takarar PDP ya yi hattara”, Ayodele

A watan Oktoba ne dai kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Nasarawa ta soke zaɓen Gwamna Abdullahi Sule, inda ta bayyana Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

A cikin watan Satumba Gwamna Sule, jigo a jam'iyyar APC ya shigar da ƙara a kotun ɗaukaka ƙara kan hukuncin na kotun zaɓe.

A ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta tanadi hukunci kan ƙarar da Sule ya shigar.

Kara karanta wannan

Daga karshe kotun daukaka kara ta fitar da muhimman takardu kan hukuncin shari'ar gwamnan Kano

Ana sa ran nan ba da jimawa ba kotun ɗaukaka ƙara za ta bayyana ranar da za ta yanke hukunci.

Ayodele a cikin wani faifan bidiyo da ya sanya a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba ya bayyana cewa:

"Bai kamata Nasarawa ta yi barci ba. Lallai ne ɗan takarar PDP ya yi taka-tsan-tsan, ya kuma ƙara himma don kada shirinsu na juya sakamakon ya zama gaskiya."
"Don haka dole ne mutumin da ake magana a kai ya yi gwagwarmaya, kada ya tsaya wasa."

An Fara Addu'o'i a Nasarawa

A wani labarin kuma, Musulmai da Kiristoci a jihar Nasarawa sun fara addu'o'i yayin da ake zaman jiran hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara za ta yanke.

Masu gudanar da addu'o'in na kwanaki bakwai sun shirya su ne domin samun nasarar ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP, David Ombugadu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng