"Ba Yan Adam Bane": Babban Malamin Addini Ya Yi Hasashen Karshen Yakin Isra'ila da Gaza
- Bishop David Oyedepo na cocin Living Faith Church Worldwide, wacce aka fi sani da Winners Chapel, ya ce ya san lokacin yaƙin Isra'ila da Hamas zai ƙare
- Malamin ya ce Allah ya gaya wa Annabi Ibrahim a cikin littafi game da Yahudawa, inda ya ƙara da cewa su ba ƴan adam ba ne
- A cewar malamin, ya bayyana cewa an tilastawa kasashe su haɗa kai da Isra'ila saboda ba ta taɓa yin rashin nasara a yaƙi ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Otta, Ogun - Bishop David Oyedepo, shugaban cocin Living Faith Church Worldwide, wacce aka fi sani da Winners Chapel, ya ce ya san lokacin da yaƙin da ake yi tsakanin Isra’ila da Hamas kan iko da zirin Gaza zai zo ƙarshe.
A cikin wani faifan bidiyo da cocin ta wallafa a shafinta na Facebook, shugabannin addinin sun bayyana Yahudawa a matsayin miyagu, inda suka ƙara da cewa Allah ya bayyana makomarsu, amma suna aiki tuƙuru don hana tabbatuwar hakan.
Oyedepo ya yi nuni da cewa babu wani cibiyoyi na soji a duniya ba tare da taimakon Yahudawa ba ya kuma yi ikirarin cewa mafi yawan manyan abubuwan ƙirkire-ƙirƙire na duniya na hannun Isra’ila ne kuma al’ummar Yahudawa ba za su taɓa yin rashin nasara a wajen yaƙi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tilasta wa mutane su haɗa kai da Isra'ila, Oyedepo
Malamin ya cigaba da cewa, an tilastawa al'ummomi su haɗa kai da Yahudawa domin za su yi duk abin da suka ce; idan suka ce za su zo su halaka ku, za su yi.
Akwai matsala: Babban malamin addini ya yi magana kan yiwuwar tsige Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa
Ya ƙara da cewa wannan wani ɓangare ne na abubuwan da Allah ya gaya wa Annabi Ibrahim game da Yahudawa kuma a cikin litattafai ya san lokacin da yaƙin Isra'ila da Hamas zai kawo ƙarshe.
A kalamansa:
Zamani bayan zamanu, wannan ƙaramar ƙasar (Isra'ila) tana damun duniya duka a yanzu. An tilasta muku yin haɗaka tare da su. Su ba mutane ba ne, kibau ne. Mafi yawan manyan abubuwan ƙirkire-ƙirƙire na zamanin Yahudawa ne."
"Wataƙila ba za ku taɓa samun kayan aikin soja a duk duniya ba tare da sa hannun Yahudawa ba. Duk waɗannan ta wurin maganar da Allah ya yi wa Annabi Ibrahim ne. Na san a cikin litattafai ƙarshen wannan yaƙin su ma sun sani amma suna ƙoƙarin yaƙar hakan ne kawai."
Fasto Oyedepo Ya Magantu Kan Sauya Jiragen Sama
A wani labarin kuma, Fasto David Oyedepo ya yi magana kan yadda ya ke sauya jiragen sama kamar keken hawa a cocinsa.
Shugaban na cocin Living Faith Church Worldwide, ya bayyana cewa hakan na daga cikin albarkar da Allah ya yi musu a cocin.
Asali: Legit.ng