Kano: Duk Da Rasa Kujerarsa a Kotu, Abba Ya Sake Yin Abu 1 Muhimmi Don Ci Gaban Al'umma
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sake mika karin kasafin kudi ta naira biliyan 24 a Majalisar jihar a yau
- Gwamna Abba Kabir ya roki Majalisar da ta amince da kudurin kasafin saboda muhimmancinshi ga al'umma
- Wannan na zuwa ne bayan kwarya-kwaryar kasafin biliyan 58 a watan Satumba wanda yanzu haka ya kai biliyan 350
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya gabatar da karin kasafin kudi har naira biliyan 24 ga Majalisar jihar.
Gwamna Abba ya mika kasafin ne a yau Talata 21 ga watan Nuwamba a dakin Majalisar jihar don neman amincewarta.
Mene Abba Kabir ke bukata a Majalisar?
Gwamnan ya gabatar da rokon ne a cikin wata sanarwa da kakakin Majalisar, Isma'il Falgore ya karanta a zaman Majalisar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Falgore ya ce Gwamna Abba Kabir ya bukaci amincewar Majalisar kamar yadda sashin 122 na tsarin dokar 1999 ya tanadar.
Daily Trust ta tattaro cewa gwamnan ya mika biliyan 58 a watan Satumba ga Majalisar don neman amincewarsu.
Mene martanin Majalisar kan kasafin?
Falgore ya ce:
"Kudurin kasafin kudi a karo na biyu na wannan shekara ta 2023 ya zama dole saboda muhimmancinsu da kuma kudaden da jihar ke sa ran samu."
Gwamnan ya bukaci sahalewar Majalisar ce bisa ga muhimmancin kasafin da kuma ayyukan raya kasa.
An gabatar da kudurin kasafin kudin a bangarori da dama da su ka hada da biyan giratuti na naira biliyan hudu, cewar New Telegraph.
Sauran sun hada naira biliyan 20 da aka ware don manyan ayyuka inda kasasfin a yanzu ya kai naira biliyan 350 bayan karin biliyan 58 a baya.
Abba ya shirya biyan 'yan fansho
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya ware fiye da biliyan shida don biyan hakkin ma'aikata a jihar.
Gwamnan ya ce zai biya ma'aikatan da su ka mutu yayin da su ke aiki hakkokinsu a jihar don yaye wa iyalansu bakin ciki.
Har ila yau, gwamnan ya soki gwamnatin da ta shude wurin azabtar da ma'aikata yayin da su ke aiki.
Asali: Legit.ng