Mataimakin Shugaba Tinubu ya sa labule da Ɗangote da wasu manyan kusoshi a Villa, bayanai sun fito
- Sanata Ƙashim Shettima na ganawa da shugabannin ɓangaren masu zaman kansu a fadar shugaban ƙasa da ke birnin Abuja
- Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote da Tony Elumelu na cikin waɗanda suka halarci ganawa da mataimakin shugaban ƙasa
- Har kawo yanzu babu cikakken bayani kan maƙasudin wannan zama wanda aka yi yau Litinin, 20 ga watan Nuwamba, 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima na ganawa da shugabannin kamfanoni masu zaman kansu a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.
Gidan talabijin na Channels ya tattaro cewa daga cikin waɗan da suka halarci taron a Villa har da shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote Group, Alhaji Aliko Ɗangote.
Haka nan kuma mamallaki kuma shugaban gidauniyar Tony Elumelu (Tony Elumelu Foundation), Mista Tony Elumelu, na cikin waɗanda suka halarci ganawa da Shettima.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa taron, wanda ya gudana a sirrince ya samu halartar Miniatan lafiya, Dokta Muhammad Ali Pate.
Sauran manyan ƙusoshin da suka halarci wannan zama da mataimkin shugaban ƙasa sun haɗa da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.
Daga cikin su har da daraktan bankin duniya a Najeriya, Schubham Chaudhuri, da dai sauransu, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Abinda Shettima ya faɗa a taron
A jawabinsa na wurin taron, mataimakain shugaban kasa, Shettima ya jaddada buƙatar gwamnati da sauran abokan hulɗa su zuba hannu jari wajen ci gaban al'umma.
A cewarsa ta haka ne kaɗai za a samar ma'aikata masu kwarewa da hazaƙa wadanda ba wai za a sha burtu da su a suniya ba, zasu zo daidai da zamanin ƙarni na 21.
Shettima ya kuma jinjinawa manyan attajiran guda biyu, Ɗangote da Elumelu, bisa la'akari da gagarumin gudummuwa da tasirin da suke da shi a cikin al'umma.
Gwamnan Benue ya lallasa PDP a Kotu
A wani rahoton na daban Kotun ɗaukaka ƙara ta kori ƙarar jam'iyyar PDP ta ɗan takararta kan zaɓen gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia.
Ta ce masu shigar da ƙara sun gaza gamsar da kotu kan ikirarin jabun takardu da suke zargin mataimakin gwamna, Samuel Ode.
Asali: Legit.ng