Mutum 1 Ya Rasu Yayin da Matasa Suka Yi Fito Na Fito da 'Yan Bindiga Bayan Sun Yi Yunkurin Kai Hari
- Wasu matasa a jihar Sokoto sun yi fito na fito da miyagun ƴan bindiga lokacin da suka yi yunƙurin kai musu farmaki a ƙauyensu
- Ƴan bindigan dai sun yi yunƙurin kai farmakin ne a ƙauyen Kwakwala da ke bayan babbar harabar jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto
- Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da cewa mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wasu kuma suka samu raunuka a yayin artabun
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Wani mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wasu matasa suka fafata da ƴan bindiga bayan sun yi ƙoƙarin kai musu farmaki a ƙauyensu a jihar Sokoto.
Ƴan bindigan dai sun yi ƙoƙarin farmakar ƙauyen Kwakwala da ke a bayan babbar harabar jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto (UDUS) a ranar, Asabar, 18 ga watan Nuwamba, cewar rahoton The Punch.
Tashin hankali yayin da rikicin manoma da makiyaya ya barke a jihar Kano, mutane da dama sun jikkata
Rundunar ƴan sanda jihar Sokoto wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta bayyana cewa mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da matasan suka yi artabu da ƴan bindigan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, Ahmad Rufa’i, ya ce ƴan bindigan a lokacin da suka yi yunƙurin farmakar ƙauyen Kwakwala a cikin birnin Sokoto, sun yi artabu da matasan yankin.
A kalamansa:
"Bisa rahoton da muka samu, ƴan bindigan da ake zargin sun kai kimanin mutum 10 ɗauke da adduna da bindigogi sun kai hari a bayan babbar harabar jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto.
"Matasan yankin sun daƙile hare-haren kuma ana cikin haka ne ƴan bindigan suka harbe ɗaya daga cikin matasan mai suna Usman wanda ya mutu nan take."
"Wasu matasa huɗu na ƙauyukan Kwalkwala da Dundaye suma sun samu raunuka daban-daban a harin.”
Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayar da tabbacin cewa rundunar a ƙarƙashin jagorancin CP Ali Kaigama, na yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da kama masu laifin.
Ƴan Bindiga Sun Halaka Matar Aure da Jaririyarta
A wani labarin kuma, wata matar aure tare da jaririyarta sun rasa rayukansu bayan ƴan bindiga sun buɗe wa motarsu wuta a jihar Sokoto.
Ƴan bindigan dai sun buɗe wa motar wuta ne lokacin da ake tafiya da matar auren zuwa asibiti tare da tagwayen jariranta bayan ta haihu a gida.
Asali: Legit.ng