Tinubu: Yadda Zan Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU a Jami’o’in Gwamnati a Najeriya
- Idan Bola Ahmed Tinubu ya na rike da shugabancin Najeriya, babu maganar yajin-aikin kungiyar ASUU a jami’o’i
- Shugaban kasar ya halarci taron yaye daliban jami’ar FUTO, ya dauki alkawarin zai kawo cigaba a manyan makarantu
- Farfesa King-David Terna Yawe ya wakilci Tinubu a wajen taron, yake cewa za a dauki matakan hana shiga yajin aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa Najeriya niyyar gwamnatin tarayya na magance yajin-aiki a jami’o’in gwamnati.
A yau Tribune ta rahoto cewa Bola Ahmed Tinubu ya ce za a rika bin duk wasu matakai na lalama kafin a bari a tafi yajin-aiki a jami’a.
An wakilci Tinubu wajen yaye dalibai a jami'ar FUTO
Shugaban kasar ya yi wannan bayani wajen yaye daliban jami’ar tarayya ta Akure, kwanaki bayan ya yarda a biya ASUU albashinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin kawo cigaba a harkar ilmi ganin yadda ake ta yawan fama da yajin-aikin ‘yan kungiyar ASUU.
Tsohon shugaban kungiyar likitocin fida na Afrika ta yamma, Farfesa King-David Terna Yawe ya wakilci Bola Tinubu a jami’ar FUTO.
A cewar King-David Terna Yawe a madadin Mai girma shugaban kasa, hadin-kan gwamnati da ma'aikata zai inganta karatun jami’a.
Gwamnatin Tinubu ta fara gyara a jami'a
The Nation ta rahoto Tinubu ya na mai cewa ya san kalubalen da ake fuskanta, ya ce saboda haka ya fito da tsarin bada bashi a jami’o’i.
"Wannan doka za ta taimakawa dalibai marasa karfi da ke jami’o’inmu wajen samun bashin karatu ba tare da ruwa ba, wanda za su biya daga baya idan sun fara aiki.
A karkashin kulawa ta, kamar yadda na fada a alkawarina, babu dalibin da zai bar makaranta a dalilin gaza biyan kudin makaranta.
- Bola Tinubu
Kiran Tinubu ga daliban jami'ar FUTO
Tinubu ya dauki alwashi gwamantinsa ba za ta yi kasa a gwiwa wajen sauke hakkinta ba, ya ce hukumomin ilmi za su yi aikinsu da kyau.
A karshe shugaban ya taya wadanda su ka kammala karatu a jami’ar murnar wannan nasara, ya nemi su yi amfani da ilmin da su ka koya.
Sanusi II ya soki Gwamnatin Buhari
Ana da labari cewa tsohon gwamnan bankin CBN, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya soki shekaru 8 na mulkin Muhammadu Buhari a Najeriya.
Kudin da gwamnatin tarayya ta karba a matsayin aro daga CBN ya kai N22.7tr masana tattalin arziki irinsu Sanusi II dai sun soki lamarin.
Asali: Legit.ng