Kwace Kujerar Abba Na Jihar Kano Alama Ce Ta Tinubu Zai Samu Tazarce a 2027, Jigon PDP, Omokri
- Wani jigo a jam'iyyar PDP, Reno Omokri, ya bayyana irin tasirin da korar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ke da shi a siyasar kasar
- Omokri ya ce hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke na nufin cewa shugaba Bola Tinubu zai samu tazarce idan ya tsaya takara a 2027
- A cewar Omokri, hakan zai faru ne saboda Kano ce ta fi kowacce jiha yawan masu kada kuri'a kuma za ta bai wa Tinubu kuri’u akalla miliyan biyu a 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Reno Omokri, tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa Jonathan, ya mayar da martani ga hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta tabbatar da korar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.
Omokri ya ce korar Gwamna Yusif ya tabbatar da sake zaben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu karo na biyu a 2027.
Ya ce jihar Kano za ta iya bai wa Tinubu kuri’u akalla miliyan biyu a zaben shugaban kasa na 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan LP da NNPP ba su hade da PDP ba, Tinubu zai samu tazarce - Mokri
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter) @renoomokri, ya shawarci jam'iyyar Labour da New Nigeria People's Party (NNPP) su bi shawarar Atiku Abubakar na hade wa da jam'iyyar PDP.
A cewar Omokri, gazawar jam’iyyun LP da NNPP na hadewa da PDP zai sa shugaba Tinubu ya samu tazarce idan ya sake tsayawa takara, kamar yadda Legit ta ruwaito.
Omokri ya ce:
“Korar Gwamna Abba Yusuf na Kano da Kotun Daukaka Kara ta yi ya kara tabbatar da nasarar Bola Tinubu a zaben 2027."
"Me ya sa? Saboda Kano ce ta fi kowace jiha yawan masu kada kuri'a, kuma za ta ba wa ‘yan takarar Shugaban kasa kuri’u akalla miliyan biyu a 2027."
Ya kara da cewa:
"Idan jam’iyyun NNPP da Labour Party sun san abin da zai amfane su, to su hade da PDP kamar yadda Waziri Atiku ya bayar da shawara."
"Domin idan ba su hade ba, to Tinubu zai sake cin zabe, wannan aikin hankali ne kawai, duk da cewa ba kowa ne ke amfani da hankali a siyasar Najeriya ba”.
Kotun daukaka kara ta tsige Gwamna Abba Kabir na jihar Kano
Idan ba ku manta ba, kotun ɗaukaka kara mai zama a babban birnin tarayya Abuja ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng