Dakarun Sojoji Sun Cafke Wani Tantirin Mai Ba Yan Ta'addan ISWAP Bayanai a Borno

Dakarun Sojoji Sun Cafke Wani Tantirin Mai Ba Yan Ta'addan ISWAP Bayanai a Borno

  • Dubun wani tantirin mutum mai ba ƴan ta'addan ISWAP bayanai ta cika a ƙaramar hukumar Monguno ta jihar Borno
  • Dakarun sojoji na atisayen 'Operation Hadarin Daji' sun yi caraf da tantirin mutumin mai suna Aji Dala wanda ke da shekara 45 a duniya
  • An dai cafke shi ne ɗauke da wata wasiƙa wacce ƴan ISWAP suka rubuto suna barazanar kawo hari a garin Monguno

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojoji na sashi na uku na atisayen 'Operation Hadin Kai' da rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) sun kama wani mai ba ƴan ta’adda bayanai mai suna Aji Dala mai shekara 45 a ƙaramar hukumar Monguno.

An tattaro cewa rundunar sojin bataliya ta 242 tare da haɗin gwiwar jami’an leken asiri ne suka kama wanda ake zargin a unguwar Charamari da ke garin a ranar 14 ga watan Nuwamban 2023.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun halaka babban malamin addinin da suka sace bayan karɓar kuɗin fansa a Kogi

Sojoji sun cafke mai ba yan ta'adda bayanai a Borno
Dakarun sojojin sun cafke tantirin ne a garin Monguno Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

A cewar Zagazola Makama, an kama shi ne dangane da wata wasiƙar barazana da aka ce ta fito daga ƴan ta'addan ISWAP a shirin su na kai hari garin Monguno a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun wani Amir Hallat Muhammed na cewa:

"Mutanen Monguno ku shirya. Mu (ISWAP) za mu kawo muku hari ranar Laraba."

Wasiƙar dai ta haifar da firgici a tsakanin mazauna garin Monguno duk da cewa daga baya an gano cewa ƙungiyar ISWAP ta rubuto wasiƙar ne domin tayar da hankula.

Sojoji sun shirya fatattakar ƴan ta'adda

Wata majiyar soji ta yi watsi da barazanar, inda ta ce sojoji a shirye suke su tunkari duk wata barazana.

"Sun yi ƙoƙari a baya kuma sun kasa cin nasara. Su gwada su gani. Monguno shine maƙabartar su. Su da kansu sun san hakan." A cewar majiyar.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun halaka mutum 2 tare da sace babban malamin addini a jihar Kwara

Sojoji Sun Halaka Ƴan Ta'addan ISWAP

A wani labarin kuma, dakarun sojojin sama na Najeriya sun halaka aƙalla ƴanta'addan ISWAP mutum 100 a wani luguden wuta da suka yi musu a Borno.

Sojojin sun kai harin ne a lokacin da ƴan ta'addan ke ganawa a dajin Bukar Mairam a ƙaramar hukumar Marte ta jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng