“Ba zan daina sonka ba”: Matashiya ta nunawa duniya saurayinta dan wada

“Ba zan daina sonka ba”: Matashiya ta nunawa duniya saurayinta dan wada

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da ta baje kolin saurayinta wanda ya kasance wada
  • Da take zuzuta shi, matashiyar ta bayyana mutumin a matsayin 'lamba ta daya', cewa mutane na iya fadin duk abun da suke so
  • Mutane da dama sun taya matashiyar murna da wannan kwarin gwiwa nata, inda wasu suka ce ba zai ci amanarta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiya yar Najeriya, @dammygold3063, ta baje kolin saurayinta dan wada a dandalin soshiyal midiya.

@dammygold3063 ta yada wani bidiyo da ke kunshe da hotunansu da dama yayin da suke nunawa juna so da kauna.

Budurwa da saurayinta dan tsurut
“Ba zan daina sonka ba”: Matashiya ta nunawa duniya saurayinta dan wada Hoto: @dammygold3063
Asali: TikTok

Ta godema sahibin nata kan duk abubuwan da ya yi mata, cewa ba za ta daina sonsa ba. Ta bayyana shi a matsayin namiji daya tamkar da dubu.

Kara karanta wannan

Dan caca da ya ciyo N102m zai taimakawa dalibin da yayi asarar kudin karatunsa a caca

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A barsu su fadi abun da suke so har yanzu kaine lamba ta daya a gareni," ta yi wa bidiyon take.

Matashiyar da sahibin nata sun rungume juna yayin da suke murmusawa a gaban kamara, cikin daya daga hotunan da ta baje.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Barbie ta ce:

"Na tayaki murna yarinya a inda ka samu so a nan farin ciki yake."

Adwoaaa ya ce:

"Ka ji tsoron dan adam da ke al'ada duk shekara."

abiodun ya ce:

"Ki dai dauki dan babinki a kafadarki."

Martha ta ce:

"Kin taki sa'a yar'uwa, ba za ki dunga gasa ba a aurenki, kuma wannan ne ainahin zaman lafiyar."

_Alajokeoge ta ce:

"Kin taki sa'a babu wanda zai hada kafada da ke a kansa @—CARDI."

kanya ta ce:

Kara karanta wannan

"Mijina ya gaza biya mun buƙata, yana zargi na da zina" Matar aure ta nemi saki a Kotu

"Allah ya albakace ku da soyayyarku. Allah ya azurta ki da sahibinki da rayuwar farin ciki."

Matar da ta auri wada ta haihu

A wani labarin, mun ji cewa wata mata ta baje kolin juna biyu da take dauke da shi sannan ta sanar da cewar ita da mijinta sun samu 'karuwa.

Kahboh Patience Fokong ta ce Allah ya azurta ta da mijinta da haihuwar diya macve.

Patience ta garzaya dandalin Facebook domin wallafa hotunanta a lokacin da take dauke da juna biyu, tana mai baje kolin yadda cikin ya amsheta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng