Yajin Aiki: Gwamna Ya Yi Karin Haske Kan Silar Jibgar Shugaban Kungiyar NLC a Imo

Yajin Aiki: Gwamna Ya Yi Karin Haske Kan Silar Jibgar Shugaban Kungiyar NLC a Imo

  • Gwamna Hope Uzodinma ya ce akwai takaici a game da da ya faru da Joe Ajero a jihar Imo a makon da ya gabata
  • Mai girma Gwamnan ya zargi shugaban NLC da yin katsalandar a harkar siyasa a lokacin ana shirye-shiryen zabe
  • Hope Uzodinma ya karyata zargin da ake yi masa na kin biyan ma’aikata albashi na tsawon watanni 31 a jihar Imo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Imo - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya yi magana a game da rikicinsa da Joe Ajaero wanda shi ne shugaban ‘yan kungiyar NLC.

Kamar yadda rahoton ya zo a Premium Times, Mai girma gwamnan ya fayyace abin da ya yi sanadiyyar yajin-aikin da aka shiga a kasar.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Shugaba Tinubu Ya Fusata, Ya Ce Matakin ‘Yan kwadago Ya Sabawa Doka

Gwamnan Jihar Imo
Gwamnan Imo ya tabo batun NLC Hoto: Hope Uzodimma @Hope_Uzodimma1
Asali: Twitter

Yayin zantawa da wasu dattawan Ibo da su ka kai masa ziyara a gidan gwamnati, Hope Uzodinma ya alakanta sabanin da adawar siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC: Rikicin Joe Ajaero da Gwamnan Imo

Gwamna Uzodinma ya nuna takaicinsa kan zarafin Joe Ajaero da aka ci da ya ziyarci Imo ana saura 'yan kwanaki ayi zaben da APC za ta ci.

"Amma duk da haka, Mai girma gwamnan ya nuna akwai laifin shugaban kungiyar kwadagon kasar da ya yi gigin raina gwamnatin Imo.
Amma a daidai wannan lokaci kuma, ina mai tir da daukacin yunkurin da shugaban ‘yan kwadagon Najeriya ya yi na raina gwamnatin Imo.
Bai taba kawo ziyara ko sau daya ba, bai taba kiran gwamnan jihar a waya ba.
Amma sai ga shi ya zo nan (Imo) ya na yin taro a boye da abokan hamayyan siyasanmu. Ba za mu yarda da wannan ba, gwamanti ba za ta kyale ba.

Kara karanta wannan

Reno Omokri ya fallasa gaskiyar dalilin da yasa NLC ta shiga yajin aikin gama gari

Ba zan sallama wannan ba, babu wanda ya isa ya yi mani barazana."

- Hope Uzodinma

Ana biyan ma'aikata albashi a jihar Imo?

Rahoton ya ce Gwamna Uzodinma wanda ya lashe zaben tazarce a makon jiya ya ce babu wasu ma’aikata da su ke bin gwamnati bashin albashi.

A cewar Gwamna, wadanda ba a biya albashin watanni ba, wasu tsirarun ma’aikata ne da su ka samu matsalar canjin wurin aiki da makamantansu.

Shari'ar zaben Gwamnoni a kotu

Idan aka koma siyasa, an ji labari Gwamnonin Jihohin Kano, Nasarawa, Filato suna fuskantar barazanar shari’a bayan sun lashe zaben da aka yi.

‘Yan Kwankwasiyya sun samu kwarin gwiwa da su ka dawo da duka kujerun ‘Yan majalisar tarayyansu a kotu, amma APC ma ta na sa ran nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng