Saudiyya Ta Bayyana Dalilin da Ya Sanya Ta Hana Fasinjoji 177 Ƴan Najeriya Shiga Ƙasar
- Ofishin jakadancin Saudiyya da ke Abuja ya yi ƙarin haske kan dalilin hana ƴan Najeriya 177 shiga ƙasar Saudiyya
- A cewar ofishin jakadancin fasinjojin sun saɓa dokoki da ƙa'idojin shiga ƙasar ne wajen bayanan da suka bayar domin neman biza
- Ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike domin rage aukuwar irin hakan a nan gaba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ofishin Jakadancin Saudiyya na Abuja ya yi ƙarin haske kan rahotannin da kafafen yaɗa labarai suka yaɗa game da dawo da ƴan Najeriya 264 da aka yi bayan sun shiga ƙasar.
A ranar Litinin ne gwamnatin ƙasar Saudiyya ta soke bizar dukkanin fasinjoji 264 da kamfanin jirgin sama na Air Peace ya yi jigilarsu a lokacin da suka isa ƙasar daga Kano, tare da dagewa cewa a dawo da su Najeriya.
Ƙasar ta buƙaci a dawo da dukkanin fasinjojin 264 amma daga baya ta bar fasinjoji 87 sun tsaya. Fasinjojin dai masu niyyar gudanar da aikin Umrah ne a ƙasar ta Saudiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Channels tv ta ce a wata sanarwa da a ka fitar a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, ofishin jakadancin na Saudiyya ya bayyana cewa:
"Fasinjojin da aka hana su shiga, daga baya kuma aka mayar da su inda suka fito, ba su cika sharuɗɗan shiga da kuma ƙa’idojin da suka dace da dokokin masarautar Saudiyya ba, domin sun bayar da bayanan da ba su dace ba domin samun nau'in biza wacce ba irin ta su ba, wanda aka gano hakan bayan sun isa."
"Wannan tsarin bai takaita ga ƴan Najeriya kaɗai ba, har da sauran ƴan wasu ƙasashen."
Gwamnatin Najeriya na gudanar da bincike
Hakazalika, ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, ta ce tana binciken lamarin don ganin ko an karya wasu ƙa'idojin ofishin jakadancin ko na jiragen sama, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
Mai baiwa ministan harkokin wajen Najeriya shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Yusuf Tuggar, ya ce ma'aikatar za ta tabbatar da rage aukuwar irin hakan a nan gaba.
Tinubu da Muƙarrabansa Sun Daura Haramar Umrah a Saudiyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, zai gudanar da aikin Umrah bayan ya kammala tarurruka a Saudiyya.
Shugaban ƙasan dai ya ziyarci Saudiyya ne domin halartar tarurraka da mahukuntan ƙasar domin samun hanyoyin zuba jari da gyara matatun man fetur na Najeriya.
Asali: Legit.ng