Kasar Africa Ta Biyu Ta Gayyaci Tinubu Don Halartar Babban Biki

Kasar Africa Ta Biyu Ta Gayyaci Tinubu Don Halartar Babban Biki

  • Shugaba Tinubu, zai kai ziyara kasar Guinea Bissau ranar Almis mai zuwa, domin bikin cikar kasar shekaru 50 da samun 'yancin kai
  • Wannan ita ce ziyarar aiki ta biyu da Tinubu zai yi zuwa Guinea Bissau, tun bayan zuwansa kasar a watan Yuli, inda ya halarci taron ECOWAS
  • Shugaban kasar, zai bar Saudiya zuwa Guinea Bissau, bayan shafe akalla mako daya a kasa mai tsarki da kuma gabatar da wasu ayyuka a Riyadd

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaba Bola Tinubu zai bar kasar Saudiyya ranar Alhamis zuwa Guinea Bissau, domin halartar bikin cikar kasar shekaru 50 da samun 'yancin kai.

Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasa, ya sanar da canjin jaddawalin tafiye-tafiyen Tinubu, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Uwargidar Tinubu Ta Lale Naira Miliyan 422, Ta Rabawa Marayu da Zaurawa 1700

Shugaban kasa Tinubu
Wannan ziyarar, za ta zamo ta biyu da shugaban kasar ya kai kasar Guinea Bissau tun hawansa mulki Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Sanarwar ta biyo bayan wasu ayyuka na mako guda da shugaban ya yi a Riyadh, babban birnin Saudiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ziyara Tinubu kasar Guinea Bissau karo na biyu

Tinubu ya halarci taron Saudiyya da Afirka a wani bangare na kokarin jawo hannun jarin kai tsaye daga ketare (FDI), da kuma nemo jari don gina abubuwan more rayuwa da ake bukata a kasar.

Wannan ita ce ziyarar aiki ta biyu da Tinubu zai yi zuwa Guinea Bissau.

A cikin watan Yuli, ya halarci taron shuwagabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) karo na 63, ziyarar aikinsa farko a nahiyar Afirka tun bayan hawansa mulki.

A wannan karon shugaban na Najeriya zai kai ziyara ne bisa gayyatar shugaba Umaro Embalo.

NLC ta lissafa sharudda shida na janye yajin aiki

Kara karanta wannan

"Allah ya ba ku ikon sauke nauyi", Tinubu ya taya Diri, Ododo, Uzodimma murna

Idan muka dawo kasa Najeriya kuwa, shuwagabannin kungiyar kwadago ta kasa NLC, sun bayyana wasu sharudda shida da ya zama wajibi a cika su kafin kungiyoyin kwadago a kasar su janye yajin aikin da suke yi.

Sun jera sharuddan shida a cikin wata sanarwa da suka fitar a shafin kungiyar na X (wanda aka fi sani da Twitter) ranar Talata.

Gwamnati ta gana da NLC

A wani ci gaba da samu, Legit Hausa ta samu rahoton wata ganawa da gwamnatin tarayya ta shiga da kungiyoyin kwadago a ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan lamuran tsaro, Nuhu Ribadu.

A yayin ganawar, ana sa ran za a kawo karshen yajin aikin da kungiyoyin kwadagon suka tsunduma tun ranar Talata, wanda ya jawo tsayawar komai a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.