Cin Zarafin Ajaero: Majalisar Tarayya Za Ta Saka Baki Kan Yajin Aikin Kungiyar Kwadago

Cin Zarafin Ajaero: Majalisar Tarayya Za Ta Saka Baki Kan Yajin Aikin Kungiyar Kwadago

  • Majalisar wakilai ta tarayya za ta saka baki don kawo karshen yajin aikin kungiyoyin kwadago da ake yi a fadin kasar
  • Sai dai wani bangare na majalisar na ganin babu amfanin yin hakan, illa ma akwai bukatar shigar da kungiyoyin kotu
  • Yajin aikin da kungiyoyin kwadagon suka fara a ranar Talata, ya jawo tsayawar ayyuka a fadin Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Majalisar wakilai ta tarayya na shirin saka baki kan yajin aikin da kungiyoyin kwadago suka shiga, kamar yadda kakakin majalisar, Tajudeen Abbas ya bayyana.

Mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, ta hanyar gabatar da kudirin gaggawa da ya shafi kasa, ya gabatar da bukatar ga shuwagabannin majalisar da su gaggauta magance matsalar.

Kara karanta wannan

"Adalci Muke So": NLC, TUC Sun Bai Wa FG Sharruda 6 Kafin Janye Yajin Aiki Na Gama-Gari

Majalisar Tarayya
Sai dai an samu rabuwar kawuna a tsakanin 'yan majalisar, wasu na ganin a shigar da karar kungiyar kwadagon, wasu na ganin a sasanta Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

An yi muhawara a zauren majalisa

‘Yan majalisar dai sun samu rarrabuwar kawuna a muhawarar, inda wasu suka nuna rashin amincewa da dalilin da ya sa suka fara yajin aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan suka bukaci gwamnati da ta kai karar kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC, bisa zargin kin bin umarnin kotu kan yajin aikin.

Sai dai, wasu bangaren ‘yan majalisar, sun yi kira da cewa, majalisar ta yi ruwa ta yi tsaki wajen kawo karshen lamarin, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kungiyoyin kwadagon sun fara yajin aikin ne a duk fadin Najeriya a ranar Talatar da ta gabata, kan abin da suka bayyana a matsayin wani hari da aka kai wa shugaban NLC, Joe Ajaero, a jihar Imo.

NLC ta lissafa sharudda shida na janye yajin aiki

A wani labarin, shuwagabannin kungiyar kwadago ta kasa NLC, sun bayyana wasu sharudda shida da ya zama wajibi a cika su kafin kungiyoyin kwadago a kasar su janye yajin aikin da suke yi.

Kara karanta wannan

Jerin kungiyoyin kwadago 19 da suka bi umurnin NLC na tsunduma yajin aiki a Najeriya

Sun jera sharuddan shida a cikin wata sanarwa da suka fitar a shafin kungiyar na X (wanda aka fi sani da Twitter) ranar Talata, Legit Hausa ta ruwaito.

NLC da TUC sun tsunduma yajin aiki

Kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito, kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC, sun umurci mambobinsu da su fara yajin aiki a fadin kasar, sakamakon harin da aka kaiwa shugaban NLC, Joe Ajaero.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.