Yajin Aiki: Ribabu Ya Kira Taron Gaggawa da Kungiyoyin Kwadago Na NLC da TUC, Bayanai Sun Fito

Yajin Aiki: Ribabu Ya Kira Taron Gaggawa da Kungiyoyin Kwadago Na NLC da TUC, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnatin tarayya ba ta son yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka fara ya ɗauki lokaci mai tsawo ana yinsa
  • Gwamnatin tarayya a ƙarƙashin ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin ya kira taron domin tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadagon
  • Za a gudanar da taron ne a yammacin ranar Laraba, 14 ga watan Nuwamba domin cimma matsaya kan janye yajin aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta kira taro da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC domin warware yajin aikin da ake yi a faɗin ƙasar nan.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, taron da aka shirya gudanarwa a yammacin yau Laraba, 15 ga watan Nuwamba, an kira shi ne a ƙarƙashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Jami'ar Bayero da ke Kano ta sanya dalibai cikin wani mawuyacin hali

FG za ta yi taro da NLC, TUC
Gwamnatin tarayya ta kira taro da kungiyoyin NLC da TUc kan yajin aiki Hoto: NLC HQ/ Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kungiyoyin NLC da TUC sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani a faɗin ƙasar nan a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, a matsayin martani kan dukan da aka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero da wasu a birnin Owerri na jihar Imo, a ranar 1 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Batun halin da ma'aikatan jihar Imo ke ciki na daga cikin dalilan da suka sanya ƙungiyar ƙwadagon tsunduma yajin aikin.

Bugu da ƙari, ana zargin jihar ta bayyana ƴan fansho mutum 10,000 a matsayin wadanda babu su kwata-kwata.

Dukan da aka yi wa shugaban NLC

Dukan da aka yi wa Ajaero da sauran shugabannin ƙwadago ya haɗa da cin zarafi, lalata motoci, da kuma sace-sacen kayayyaki kamar su wayoyi, kuɗi, da katin ATM.

Lamarin ya faru ne a yayin wata zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a sakatariyar NLC ta jihar Imo a ranar 1 ga watan Nuwamba. Wannan ta'asa ta janyo cece-kuce da nuna ɓacin rai a faɗin ƙasar nan da ma sauran ƙasashen duniya.

Kara karanta wannan

Yajin aikin NLC: CONUA kishiyar ASUU ta ƙi shiga yajin aiki, ta bayyana dalilanta

Yajin Aiki Ya Sanya an Mayar da Ɗalibai Gida a Legas

A wani labarin kuma, yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka tsunduma a faɗin ƙasar nan, ya sanya an mayar da ɗalibai gidajensu bayan sun je makarantu a Legas.

Ɗaliban na makarantun firamare da sakandare na gwamnati sun koma gida ne saboda yajin aikin da malaman makarantunsu suka shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng