Makarantun Gwamnati a Legas Sun Mayar Da Dalibai Gida Saboda Yajin Aikin NLC

Makarantun Gwamnati a Legas Sun Mayar Da Dalibai Gida Saboda Yajin Aikin NLC

  • An rufe makarantun gwamnati, da suka hada da firamare da sakandire a jihar Legas, biyo bayan umurnin kungiyar kwadago na shiga yajin aiki
  • Rahotanni sun bayyana cewa, dalibai sun shiga makarantu a safiyar ranar Laraba, sai dai, shuwagabannin makarantun, sun sallame su
  • Makarantun gwamnati na jihar Legas, sun rufe ne saboda bin umarnin kungiyar malamai ta Najeriya NUT wadda kungiya ce mai bin umurnin NLC

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas - Rahotannin da muke samu yanzu, na nuni da cewa, a yau Laraba, 15 ga watan Nuwamba, makarantun gwamnati a Legas suka rufe ayyukansu bisa bin umarnin kungiyar kwadago ta NLC.

A ranar litinin ne dai shuwagabannin kungiyar kwadagon Najeriya NLC suka bayar da umurni na neman ma’aikata su fara yajin aiki a fadin kasar.

Kara karanta wannan

An kama dalibin FUNAAB kan ciyar da budurwarsa guba a Ogun

Daliban makarantun gamnati a Legas
An ga dalibai suna kokarin neman abin hawa don komawa gida, wasu kuma suna shawagi a harabar makarantu Hoto: TheNationOnline
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta bayyana cewa an ga dalibai daga makarantun firamare da sakandare daban-daban na gwamnati a kan tituna, suna komawa gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu kuma daliban sun yi yawo a harabar makarantun.

Dalilin da yasa aka rufe makarantu a Legas

A wata makarantar sakandire ta gwamnati da ke unguwar Mushin a Legas, an bar kofar a bude a lokacin da dalibai ke ficewa daga harabar makarantar.

Sai dai, an hangi wasu malamai sun taru a karkashin bishiya, suna tattaunawa.

Wani malami da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa jaridar The Nation cewa, sun bi umarnin kungiyar malamai ta Najeriya (NUT) wadda kungiya ce mai bin umurnin NLC.

Jerin kungiyoyi 19 da suka tsunduma yajin aiki a Najeriya

Akalla kungiyoyi goma sha tara ne rahotanni suka bayyana cewa sun tsunduma yajin aikin da kungiyoyin kwadago na kasa suka tsunduma a fadin Najeriya

Kara karanta wannan

Yajin aikin NLC ya gamu da babban cikas a jihar Ƙaduna yayin da ma'aikata suka rabu gida biyu

A daren ranar Litinin, kungiyoyin kwadagon suka sanar da fara yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar, wanda ya fara aiki a safiyar ranar Talata, kamar yadda jaridar Legit Hausa ta wallafa.

Wannan yajin aikin, ana yin shi ne biyo bayan gazawar gwamnati na biyan bukatun kungiyoyin kwadagon, da kuma cin zarafin shugaban NLC da aka yi a Imo

Kungiyoyin sun hada da; Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU), kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU), da kungiyar malaman makarantun kwaleji (CEASU).

Sauran sun hada da; Kungiyar malaman makarantun Polytechnics (ASUP), Kungiyar ma'aikatan abin sha da taba ta kasa (NUFBTE) da Kungiyar manyan ma'aikatan makarantun Polytechnics ta Najeriya (SSANP) da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.