Uwargidar Tinubu Ta Lale Naira Miliyan 422, Ta Rabawa Marayu da Zaurawa 1700
- Uwargidar shugaba Bola Tinubu ta raba makudan kudi ga iyalan sojojin Najeriya da su ka mutu a wajen yake-yake
- Gidauniyar Oluremi Tinubu ta kashe sama da Naira miliyan 400 a kan marayun da wadannan sojoji su ka bari a duniya
- Sanata Tinubu ta na fatan matan su yi amfani da kudi domin bunkasa kasuwanci ko ya zama silar jarin fara yin sana’a
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Mutum akalla 1, 709 za su amfana da gudumuwar N250, 000 da uwargidar shugaban kasar Najeriya, Oluremi Tinubu ta raba.
Rahoton This Day ya ce matar shugaba Bola Tinubu ta yi wannan dawainiya karkashin gidauniyarta, Renewed Hope Initiative (RHI).
Kokarin Remi Tinubu ta Renewed Hope Initiative
Wadannan miliyoyin kudi har N427. 75m da aka rabawa yaran sojojin da su ka mutu ya na cikin kokarin da Remi Tinubu ta ke yi a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gidauniyar RHI ta na taimakawa marasa galihu tare da inganta rayuwa da jin dadin marasa hali, kwanakin baya Remi ta raba kudi a Filato.
Kamar yadda rahoton ya nuna, an zakulo marayun da zaurawa ne daga ko ina a fadin kasar nan bayan mutuwan mahaifansu a filin daga.
Jaridar The Nation ta ce Manjo Janar Danladi Salisu ya wakilci hafsun tsaro, Janar Christopher Musa wajen rabon tallafin da aka shirya.
Remi Tinubu ta tausayawa marayu
Uwargidar shugaban Najeriyan watau Remi Tinubu ta shaida cewa ta na fatan gudumuwar za ta kawowa wadannan Bayin Allah sauki.
Remi Tinubu ta kuma yi kira da sauran masu ruwa da tsaki su tuna da ‘ya ‘yan matattun a lokacin da talakawa ke kukan tsadar rayuwa.
Jawabin Sanata Remi Tinubu
"A karkashin tsarin inganta rayuwar marasa galihu na gidauniyar Renewed Hope Initiative, mun zo nan domin tallafawa zaurawa 1, 70, kowace da N250, 000.
Wannan zai kara maku jari a kasuwancin da ku ke yi ko kuwa ku iya fara sana’ar da ku ke sha’awa domin ku iya daukar nauyin iyalinku.
Kun nuna namijin kokari a cikin tsakiyar masifa, kuma mun zo ne domin mu dafa maku a yayin da ku ke kokarin fara wata sabuwar rawuya.
Wasunku sun dade su na zawarci yayin da wasu kuma ba su dade da shiha zawarcin ba kuma mu na fatan manya za su karfafi kanananku.
- Remi Tinubu
Atiku ya na so ayi waje da Tinubu
A babin siyasa kuwa, labari ya zo cewa Atiku Abubakar ya koka da salon mulkin Bola Tinubu, ya ce ana neman komawa mulkin jam’iyya guda.
Wazirin Adamawa zai so shi da Rabiu Kwankwaso da Peter Obi su hada-kai domin tunkarar Bola Tinubu ko kuwa APC ta murkushe kowa.
Asali: Legit.ng