NDIC Ta Lissafa Bankuna 20 Da Suka Rushe, Ta Bukaci Masu Ajiya Su Taho Su Karbi Kudadensu
- Hukumar Inshorar masu ajiyar kudi ta Najeriya (NDIC) ta bayyana sunayen wasu bankuna 20 da suka gaza, sannan za ta biya wadanda suka yi ajiyar kudi a bankunan
- Hukumar NDIC ta ce sabanin rahotannin baya-bayan nan, babu wasu sabbin bankuna da suka ruguje a Najeriya
- Hukumar ta bayyana cewa masu ajiya, masu bayar da bashi, da masu hannun jari, za su sami karin naira biliyan 16.16 a kudin da za a biya su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Masu ajiya, masu ba da bashi, da masu hannun jari na bankuna 20 da suka rushe a Najeriya za su samu karin naira biliyan 16.18, in ji hukumar inshorar masu ajiyar kudi ta Najeriya (NDIC).
Sabon biyan da za a yi, zai kara yawan ribar da aka biya masu ajiyar kudin zuwa naira biliyan 61,63 bayan biyan jimillar kudaden da suka kai naira biliyan 4545 ya zuwa watan Yulin shekarar 2023.
Wannan adadin, a cewar hukumar, ya zarce kudaden da aka ajiye a bankuna ashirin din da suka rushe, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NDIC ta karyata rahotannin sabbin bankuna da suka gaza
A cewar daraktan sadarwa na NDIC, Bashir Nuhu, bankuna 20 da suka rushe na daga cikin bankunan da aka rufe a baya, sakamakon soke lasisin gudanar da ayyukansu da babban bankin Najeriya (CBN) ya yi.
CBN ya soke lasisin bankunan ne a tsakanin shekarar 1994 zuwa 2018, kamar yadda Bashir Nuhu ya bayyana a ranar Litinin, a Abuja, a cewar rahoton Daily Trust.
Ya ce sanarwar ta biyo bayan wani rahoto da ke yawo na cewa an samu sabbin bankuna 20 da suka rushe.
Sunayen bankunan da suka rushe:
- Liberty Bank
- City Express Bank
- Assurance Bank
- Century Bank
- Allied Bank
- Financial Merchant Bank
- Icon Merchant Bank
- Progress Bank
- Merchant Bank of Africa (MBA)
- Premier Commercial Bank
- North-South Bank
- Prime Merchant Bank.
- Commercial Trust Bank
- Cooperative and Commerce Bank
- Rims Merchant Bank
- Pan African Bank
- Fortune Bank
- All States Trust Bank
- Nigeria Merchant Bank
- da kuma, Amicable Bank in liquidation.
NDIC ta fara tantance masu ajiyar kudi a bankuna
A cikin watan Afrilun wannan shekara, hukumar NDIC ta fara tantance masu ajiyar kudi a bankin Peak Merchant, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito a baya.
Wannan na daga cikin matakan da hukumar ke dauka na tabbatar da inshorar kudaden da mutane ke ajiye wa, da kuma mayar masu idan har aka samu akasi banki ya rushe.
Asali: Legit.ng