NDIC ta fara biyan masu ajiya kudadensu sakamakon durkushewar kananan bankuna 154
- Hukumar NDIC ta ce ta fara biyan masu ajiya kudadensu sakamakon durkushewar wasu kananan bankuna 154 da bankin CBN ya kwace lasisinsu a shekarar 2018
- Shugaban hukumar NDIC, Alhaji Umaru Ibrahim, ne ya fadi hakan a kasuwar bajakoli ta kasa da kasa da ke Abuja
- CBN ta kwace lasisin bankunan a karshen shekarar 2018 biyo gazawarsu da kuma rashin shugabanci mai nagarta a wajen gudanar da harkokinsu, a cewar Ibrahim
Hukumar kula da harkokin da suka shafi bankuna (NDIC) ta ce ta fara biyan masu ajiya kudadensu sakamakon durkushewar wasu kananan bankuna 154 da babban bankin kasa (CBN) ya kwace lasisinsu a shekarar 2018.
Alhaji Umaru Ibrahim, shugaban hukumar NDIC, shine wanda ya fadi hakan a kasuwar bajakoli ta kasa da kasa da ke Abuja.
Shugaban, wanda Mista Mustapha Ibrahim, darekta a hukumar NDIC, ya wakilta ya ce sun fadada aikin biyan masu ajiya har zuwa wasu kananan bankuna na musamman da ake yi wa lakabi da PMBs (Primary Mortgage Banks) guda shidda.
DUBA WANNAN: A karshe: 'Yan Kwankwasiyya sun yi magana a kan zarginsu da cin mutuncin Pantami
A cewar Ibrahim, CBN ta kwace lasisin bankunan a karshen shekarar 2018 biyo gazawarsu da kuma rashin shugabanci mai nagarta a wajen gudanar da harkokinsu.
"A saboda haka ne hukumar NDIC ta dakatar da aiyukan banka kuma yanzu ta fara biyan masu ajiya kudadensu," a cewar Ibrahim.
Ya bayar da tabbacin cewa hukumar NDIC za ta cigaba da kara zage dantse wajen karbar korafin masu ajiya da waware matsalolinsu da bankunansu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng