'Yan Bindiga Sun Tare Motar Gwamnatin Jihar Arewa, Sun Tafka Mummunar Ɓarna Tare da Sace Mutane
- Miyagun ƴan bindiga sun sace mutane 13 daga motar kamfanin sufuri ta Gwamnatin jihar Benuwai
- Shaidu sun bayyana cewa maharan sun tare motar Bas ɗin a titin Naka zuwa Makurdi ɗauke da fasinjoji 16, uku suka tsira
- Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar, SP Catherine Anene, ba ta amsa kira ko sakonnin da aka tura mata ba
Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Yan bindiga sun yi garkuwa da Fasinjoji 13 da ke tafiya a motar kamfanin sufuri mallakin Gwamnatin jihar Benuwai 'Benue Links' a kan titin Naka.
Wakilin Daily Trust ya tattaro cewa ranar Litinin wani magidanci, matarsa da direbansu suka faɗa hannun masu garkuwa a wannan hanya ta Naka wadda ta lalace.
Ganau sun bayyana cewa Fasinjojin sun taso ne daga Otukpo zuwa Makurɗi a motar Benue Links, kwatsam a daidai titin Naka, ƙaramar hukumar Gwer, ƴan bindiga suka tare su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutum uku kaɗai suka tsira
Ɗaya daga cikin waɗanda abun ya faru a kan idonsu ya ce Motar na ɗauke da mutane 16 lokacin da maharan suka tare su ranar Alhamis, mutum uku kaɗai suka tsira.
Ya ce ƴan bindigan sun tattara sauran mutane 13, sun tafi da su zuwa cikin daji. Lamarin ya faru ranar 9 ga watan Nuwamba a kauyen Tyolaha Ahume da ke tirin Naka-Makurɗi.
Manajan kamfanin sufurin Benue Links, Kwamared Alexander Fanafa, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho cewa ƴan ta'adda sun tare motarsu a hanyar Naka.
Amma Fafana ya bayyana cewa a halin yanzu ba shi da cikakken bayani kan abin da ya faru a harin wanda ya rutsa da motar Bas mallakin Gwamnatin jihar Benuwai.
Yayin da aka tuntuɓe ta, jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Benuwai, SP Catherine Anene, ba ta ɗaga kiran waya ko amsa sakonnin da aka tura mata ba, Vanguard ta ruwaito.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugabar Karamar Hukuma
A wani rahoton na daban Yan bindiga sun yi garkuwa da shugabar ƙaramar hukumar Okpokwu da aka dakatar a jihar Benuwai, Amina Audu.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun sace matar ne yayin da take hanyar Naka zuwa Makurdi da safiyar ranar Litinin.
Asali: Legit.ng