Yajin Aiki: Shugaba Tinubu Ya Fusata, Ya Ce Matakin ‘Yan kwadago Ya Sabawa Doka

Yajin Aiki: Shugaba Tinubu Ya Fusata, Ya Ce Matakin ‘Yan kwadago Ya Sabawa Doka

  • A sakamakon yajin-aikin da ma’aikata su ka shiga a duk Najeriya, Fadar shugaban kasa ta maidawa NLC da TUC martani
  • Bayo Onanuga ya zargi shugabannin kungiyoyin kwadago da rashin yi wa kotu biyayya bayan Alkalin NIC ya haramta yajin-aikin
  • Gwamnatin tarayya ta zargi shugabannin ma’aikatan da azabtar da miliyoyin jama’a saboda abin da ya faru da Joe Ajaero a Imo

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi tir da kungiyoyin NLC da TUC da su ka dage sai sun tafi yajin-aiki bayan abin da ya faru da Joe Ajaero.

Mai taimakawa shugaban kasa a yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya ce ‘yan kwadago sun wuce gona da iri a damar da su ke da ita.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta dauki gagarumin mataki yayin da aka fara yajin aikin gama gari

A Twitter Onanuga ya maida martani ya na cewa babu dalilin tafiya yajin-aiki a kasar.

'Yan kwadago
Shugabannin 'yan kwadago sun jawo yajin-aiki Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin Tinubu ya soki yajin-aikin NLC

Hadimin shugaban kasar ya na ganin gadara kurum ta jawo kungiyoyin ma’aikatan ke neman yaudarar gwamnati da kuma takurawa al’umma.

A cewar mai ba shugaban Najeriyan shawara, za a azabtar da mutane fiye da miliyan 200 saboda kurum sabanin mutum da mutum da aka samu.

Baya ga haka, Onanuga ya ce NLC da TUC sun yi wa kotu rashin biyayya da zuwa yajin-aikin, ya ce hakan ya nuna ba su girmama shari’a.

Mun yi takaicin jin matakin NLC da TUC na kiran ‘ya ‘yansu su shiga yajin-aiki daga tsakar dare duk da hukuncin Benedict Backwash Kanyip a kotun ma’aikata.

Matakin nan na kungoyoyin NLC da TUC kokarin nuna gadara ne, kuma karara yake cewa babu dalilinsa. Shugabannin NLC na neman taso gwamnati a gaba ne.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: ASUU tayi umarnin yajin aiki, malaman jami’a sun yi wa NLC biyayya

NLC: Joe Ajaero ya jawowa kan shi - Onanuga

Leadership ta ce jawabin ya nuna kuskuren da Kwamred Joe Ajaero ya yi ne ya haifar masa da abin da ya faru da shi mara dadin ji a jihar Imo.

Fadar shugaban kasa ta zargi shugabannin NLC da kokarin tunzura ma’aikatan Imo su shiga yajin-aiki na babu gaira-babu dalili, a karshe aka doke shi.

NLC da TUC sun fara yajin-aiki

Cikin tsakar daren yau ne kungiyoyin NLC da TUC su ka shiga yajin-aiki a ko ina a fadin kasar nan kamar yadda labari ya gabata tun kafin yanzu.

Abin da ya fusata ma’aikatan shi ne ba a cafke wadanda su ka lakadawa Festus Osifo duka a Imo, 'yan kwadago sun ce ba a dauki wani mataki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng