Wani Mutum Ya Nunawa Duniya Gidan da Ya Yi Rayuwa Tsawon Shekaru 7 Kafin Ya Zama Mai Arziki
- Wani matashi ya ba da labari mai ban mamaki kan yadda ya tashi daga gidan talakawa zuwa hadadden gida bayan shafe shekaru bakwai yana aiki tukuru
- Ya ce bai taba yanke kauna ba cewa rayuwa za ta inganta a gare shi kuma cewa mafarkinsa zai zama gaskiya
- Bidiyon ya kuma nuna sabon gidansa, wanda aka yi wa ado da kayan alatu kuma ya fi na baya ababen more rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wani matashi ya bayyana yadda ya sauya irin rayuwar da yake yi daga zama a gidan talakawa zuwa wani mai dankaren kyau bayan shafe tsawon shekaru bakwai yana fadi tashi.
Ya ce a koda yaushe yana tunani mai kyau sannan ya sanya a ransa cewa rayuwa za ta inganta gare shi kuma mafarkinsa zai zama gaskiya.

Kara karanta wannan
Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

Source: TikTok
Bidiyon ya baje kolin sabon gidansa, wanda aka kawata sosai kuma ya fi na baya ababen more rayuwa a ciki.
Kalli bidiyon a kasa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jama'a sun yi martani kan sauyin da matashi ya samu a rayuwa
Legit Hausa ta tattaru wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:
Cyndi ta ce:
"Allah sai yaushe? Ina so na share hawayen mahaifiyata."
User636363836 ya rubuta:
"Hatta ga tsohon gidan yana da kyau shima."
Anondecherryb ta yi martani:
"Na tayaka murna dan uwa. Allah ne gaskiya a rayuwa."
IhenwaPrecious:
"Na tayaka murna, na san daya daga cikin iyayengijina za su yi mun irin haka da dangi na."
I'mSomtoochukwu:
"Na tayaka murna ina yi wa dangina ma fatan samun irin wannan."
JulietAkpabio:
"Allah zai kara azurtaka fiye da wannan."
Divineuzoma278:
"Na tayaka murna nima haka labarina zai kasance Amin."
Joybeautiful28:
"Na tayaka murna dan uwa."
Matashi ya dankara gida na zamani
A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya mai suna @bansi342 wanda duniya bata san irin sana’arsa ba yake yi ba ya baje kolin katafaren gidan da ya ginawa kansa.
Da yake wallafa bidiyon gidan a yanar gizo, matashin ya girmama batun mallakan gida fiye da kashe miliyoyin kudi kan motoci. Ya yi bidiyon cikin harabar gidan nasa wanda ke babur fake a cikinsa.
A wani bidiyon kuma, matashin ya bayyan cewa ya gamsu da yadda yake kashe kudadensa. Ya kawata gidan ta yadda kana ganinsa z aka san kudi ya yi kuka.
Asali: Legit.ng
