Kungiyoyin Kwadago Sun Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani Kan Lakadawa Shugaban NLC Duka
- Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa kungiyoyin kwadago ma Majeriya sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar
- Za a fara yajin aikin ne a daren ranar Litinin, kamar yadda daya daga cikin shuwagabannin kungiyoyin kwadagon, Festus Osifo, ya bayyana
- Shiga yajin aikin, ba zai rasa nasaba da farmakin da aka kai wa shugaban kungiyar kwadago, Joe Ajaero a jihar Imo ba, inda aka lakada masa dukan tsiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC, sun umurci mambobinsu da su fara yajin aiki a fadin kasar, sakamakon harin da aka kaiwa shugaban NLC, Joe Ajaero.
Kungiyoyin kwadagon sun umurci dukkanin kungiyoyin ma'aikata da ke karkashinsu, da su tsunduma yajin aikin, bisa umurnin majalisar zartaswa ta kungiyoyin.
Shugaban TUC, Festus Osifo, wanda ya yi jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, ya ce yajin aikin zai ci gaba da kasancewa har sai “gwamnati a dukkan matakai sun farga da alhakin da ya rataya a wuyansu.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ya jawo shiga yajin aiki?
Legit ta ruwaito maku yadda shugaban kungiyar kwadago (NLC), Comrade Joe Ajaero, ya labarta yadda ya ci dukan tsiya a hannun jami'an tsaron da suka yi awon gaba da shi a ranar Laraba.
Ajaero ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafofin watsa labarai a ranar Alhamis, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Dalilin da yasa aka yi awon gaba da Joe Ajaero
Akwai rahotannin da suka bayyana cewa an yi awon gaba da Joe Ajaero daga garin Owerri, inda ya ke shirye shiryen jagorantar ma'aikata gudanar da wata zanga-zanga akan gwamnatin jihar.
Zaben Bayelsa: Bayan tattara sakamakon kananan hukumomi, an fadi wanda ke kan gaba da kuri'u dubu 65
An ruwaito cewa Ajaero na tsaka da shirin gabatar da jawabi ga ma'aikatan jihar Imo a sakatariyar NLC, wasu jami'an tsaro dauke da makamai suka mamaye sakatariyar, inda suka yi awon gaba da shi zuwa wani waje da ba a sani ba.
Kungiyoyin NLC da TUC sun kira babban taron NEC
A ranar talatar da ta gabata, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa kungiyoyin NLC da TUC sun kira taron gaggawa da nufin nazari kan yiwuwar tsunduma yajin aikin biyo bayan cin zarafin da aka yi wa shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, a jihar Imo.
A yain taron, sun tattauna da yin duba kan yarjejeniyar fahimta (MoU) da ƙungiyoyin kwadago suka rattaɓa wa hannu bayan cimma matsaya da gwamnati ranar 2 ga watan Oktoba.
A zaman taron ne, suka cimma matsayar fada wa yajin aikin a mako mai zuwa.
Asali: Legit.ng