Abba Ya Tura Dalibai Jami’o’in Kasar Waje, ASUU Ta Ce Akwai Matsaloli Dankare a Kano
- Kungiyar ASUU ta reshen YUMSUK ta koka game da yadda abubuwa su ke tafiya a mulkin Abba Kabir Yusuf
- Malaman jami’ar ta jihar Kano sun fito da kalubalen da su ke fuskanta na rashin kudi zuwa kin biyan hakkoki
- Shugaban kungiyar ta ASUU ya shaida cewa an yi dabara an hana su iya ganawa da Mai girma Abba Kabir Yusuf
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Kungiyar malaman jami’a (ASUU) ta reshen Yusuf Maitama Sule (YUMSUK) ta zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da watsi da makarantar.
Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta rahoto shugaban ASUU na jami’ar YUMSUK, Mansur Saeed ya zargi gwamnati da watsi da su.
ASUU ta koka da Abba a Kano
Shugaban na ASUU da sakatarensa sun fitar da jawabi inda su ka koka game da halin da jami’ar ta jihar Kano ta ke ciki tun bayan canjin gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mansur Saeed yake cewa sun yi kokarin ganawa da Abba Kabir Yusuf, amma an hana su, watanni kusan shida kenan da hawansa kan mulki.
Kungiyar ASUU ta ce akwai bukatar inganta halin da ma’aikatan jami’a ke ciki, kuma a sakan masu mara tare da ware kudi domin a samu cigaba.
Jawabin Shugabannin kungiyar ASUU
"Mu na sanar da al’umma da nufin wayar da kai kan matsalar da ta ke dankare da kuma tabarbarewar jami’o’i saboda rashin kulan gwamnati."
- Mansur Sa'eed
Kungiyar ta na kira da ayi gaggawan kafa majalisar da ke kula da jami’ar tare da biyan ragowar kudin alawus na EAA da sauran bashin hakkoki.
The Cable ta ce kungiyar ASUU ta bukaci ayi gaggawan amincewa da amfani da tsarin albashin da gwamnatin tarayya ta fito da shi daga Junairu.
Sauran bukatun ASUU a Jihar Kano
Ba a nan kadai bukatun su ka tsaya ba, malaman suna so gwamnatin Kano ta biya su bashin N35, 000 da gwamnatin tarayya ta fara biya.
Solacebase ta ce shugabannin kungiyar ASUU sun nemi a dakatar da cire 25% daga asusun jami’o’i, ta ce ba a aiko mata kudin ayyuka.
ASUU ta na so Abba Kabir Yusuf ya dage wajen ganin TETFund ta dauki dawainiyar karatun malamai a jami’o’in gida da na kasashen waje.
Kokarin gwamnatin Kwankwasiyya a Kano
Kwanaki aka ji Gwamnatin Kano ta dawo da tsarin Kwankwasiyya na kai dalibai karatu a kasar waje, yanzu matasa da-dama suna ketare.
Bayan nan an ji jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso ya ce zai ɗauki nauyin mahaddata Alƙur'ani da ke Kano su samu ilmi na zamani.
Asali: Legit.ng