Jimami Yayin da Shahararren Malamin Addini Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ya Na da Shekaru 103
- Ana cikin jimami bayan rasuwar shahararren Fasto mai suna Samuel Abidoye a jihar Kwara a jiya Lahadi
- Abidoye wanda aka fi sani da Baba Aladura har ila yau, shi ne shugaban cocin Cherubim da Seraphim da ke fadin duniya
- Sakataren cocin, Ademola Odetundun shi ya sanar da mutuwar Faston a cikin wata sanarwa a jiya Lahadi 12 ga watan Nuwamba
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kwara - Shugaban Cocin Cherubim da Seraphim, Samuel Abidoye ya riga mu gidan gaskiya a jihar Kwara.
Faston wanda aka fi sani da Baba Aladura ya rasu ne a jiya Lahadi 12 ga watan Nuwamba ya na da shekaru 103, Legit ta tattaro.
Yaushe Fasto Baba Aladura ya rasu a Kwara?
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban sakataren cocin, Ademola Odetundun shi ya sanar da mutuwar Faston a cikin wata sanarwa a jiya Lahadi 12 ga watan Nuwamba.
Har ila yau, cocin ya tabbatar da rasuwar ga jaridar Punch a yau Litinin 13 ga watan Nuwamba.
Olatundun a cikin sanarwar ya ce Baba Aladura ya rasu da safiyar Lahadi 12 ga watan Nuwamba a gidansa da ke Ilorin a jihar Kwara.
Wane ne Fasto Baba Aladura a Najeriya?
Ya ce:
"Ya mutu cikin salama."
Yayin da cocin ya sanar da cewa za a bayyana tsare-tsaren bikin binne shi nan ba da jimawa ba.
An haifi Baba Aladura a ranar 26 ga watan Yuni a shekarar 1920 a matsayin dan Sarkin Omu Aran a karamar hukumar Irepodun da ke jihar Kwara.
Babban rashi yayin da mace Manjo Janar ta farko a Najeriya ta riga mu gidan gaskiya ta na da shekaru 84
Tribune ta tattaro cewa an dauki gawar marigayin zuwa dakin adana gawarwaki a birnin Ilorin da ke jihar Kwara.
Shahararren dan wasan kwaikwayo, Samanja ya rasu
A wani labarin, Shahararren dan wasan kwaikwayo a Arewacin Najeriya, Usman Baba Pategi ya riga mu gidan gaskiya a jihar Kaduna.
Marigayin wanda ake fi sani da Samanja mazan fama ya rasu ne a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba a gidansa da ke Kaduna.
Samanja ya yi kaurin suna a wasan kwaikwayo da aka shafe shekaru ana gudanarwa a gidan rediyon Najeriya ta Kaduna.
Asali: Legit.ng