Mutane 8 Sun Mutu, Wasu da Dama Sun Jikkata a Wani Hatsarin Jirgin Ruwa a Taraba
- Akalla mutane takwas ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani hatsarin jirgin ruwa da ya rutsa da su a jihar Taraba
- n tattaro cewa kwale-kwalen ya nufi kasuwar Anyeshi da ke jihar Benuwe daga Ibi a jihar Taraba inda hatsarin ya afku da misalin karfe 4:30 na rana
- Hukumar ta HOLGA, ta gargadi al’ummar gundumar da su daina yin tafiye-tafiyen dare a tekunan garin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Taraba - Kimanin makonni biyu baya da wani hatsarin kwale-kwale ya lakume rayuka da dama a jihar Taraba, yanzu ma mutane 8 sun mutu tare da jikkata wasu da dama a wani sabon hatsarin jirgin ruwa a karamar hukumar Ibi.
PREMIUM TIMES ta tattaro cewa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi a kauyen Anyeshi da ke kusa da jihar Benuwe.
Shugaban ma'aikatar karamar hukuma (HOLGA) a gundumar Ibi, Isa Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce sama da mutane takwas ne suka rasa rayukansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A daina tafiye-tafiyen dare a jirgin ruwa - Hukumar HOLGA
Mista Mohammed, wanda ya ce hatsarin bai faru a Taraba ba, a makwafciyar jihar Binuwai ya faru, ya ce dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin ‘yan Ibi ne.
Hukumar ta HOLGA, wadda ba ta iya tantance adadin fasinjojin da ke cikin jirgin a lokacin da hatsarin ya afku ba, ta gargadi al’ummar gundumar da su daina yin tafiye-tafiyen dare a tekunan garin.
An tattaro cewa kwale-kwalen ya nufi kasuwar Anyeshi da ke jihar Benuwe daga Ibi a jihar Taraba inda hatsarin ya afku da misalin karfe 4:30 na rana.
Wani mazaunin Ibi, Adamu Likita, wanda ya zanta da PREMIUM TIMES ta wayar tarho, ya ce yawancin wadanda abin ya shafa ‘yan yankin ne.
Gwamnan Taraba ya magantun kan faruwar hatsarin
A wani bangaren kuma, gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya bayyana kaduwarsa kan faruwar lamarin.
Gwamnan, a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Emmanuel Bello, ya fitar, ya bayyana hatsarin kwale-kwalen a matsayin iftila'i, wanda ya zo jim kadan bayan faruwar irin hakan a Karim Lamido.
Ya jajantawa al'ummar Ibi, ya kuma yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.
Jirgin ruwa dauke da mutane fiye da 100 ya kife a Taraba
Makonni biyu da suka gabata, mun kawo maku rahoton yadda jirgin ruwa dauke da fasinjoji sama da 100 ya kife a tsakiyar ruwa a Rafin Benue a ranar Asabar.
Yan kasuwa, mata da yara da ke hanyar zuwa garin Binnari da ke karamar hukumar Karim-Lamido na jihar na cikin jirgin ruwan da abin ya faru da shi.
Asali: Legit.ng