Tashin Hankali Yayin da Aka Caka Wa Mata Wuka Har Lahira a Wurin Ibada Yayin Raba Fada, an Yi Bayani

Tashin Hankali Yayin da Aka Caka Wa Mata Wuka Har Lahira a Wurin Ibada Yayin Raba Fada, an Yi Bayani

  • Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta tabbatar faruwar wani iftila’i inda aka caka wa wata mata wuka har lahira a jihar
  • Marigayiyar mai suna Rachel Johnson ta gamu da ajalinta ne yayin da take kokarin raba fada a coci yayin da mambobin ke rikici
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce wanda ake zargin ya tsere

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas – Wata mata ta gamu ajalinta yayin raba fada a coci lokacin da ake kazamin rikici a jihar Legas.

Matar mai suna Rachel Johnson ‘yar shekaru 47 an caka mata wuka ne har lahira yayin da take raba fada tsakanin mambobin cocin a yankin Abaranje.

Kara karanta wannan

Kogi: Jimami yayin da shahararren dan siyasar APC ya riga mu gidan gaskiya awanni kadan kafin zabe

An caka wa wata mata wuka yayin raba fada a wurin ibada a Legas
'Yan sanda sun yi martani kan kisan matar a Legas. Hoto: NPF Lagos.
Asali: Facebook

Yaushe kisan ya faru a cocin jihar Legas?

Wani babban jami’in dan sanda ya bayyana cewa da misalin karfe 3:00 na asuba mijin matar ya kawo rahoto ofishin ‘yan sanda, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mijin matar mai suna Okerube Johnson ya ce matar ta je cocin inda ta ci karo ana fada yayin da ita kuma ta yi kokarin shiga tsakani.

Johnson ya ce yayin da take kokarin raba fadar ce wani daga cikin ya caka mata wani abu mai kaifi inda a take ta fara zubar da jini.

Mene mijin marigayiyar ke cewa kan kisan a Legas?

Ya ce:

“An dauke ta zuwa babban asibitin Igandu amma duk da kokarin likitoci don ceto rayuwarta ya ci tura inda ta mutu a asibitin.
“An ajiye gawarta a dakin gawarwaki a babban asibitin Mainland da ke Yaba don yin bincike.”

Kara karanta wannan

Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Benjamin Hundeyin ya yi martani kan lamarin da ya faru a cocin, News Headlines ta tattaro.

Ya ce:

“Wanda ake zargin ya tsere kuma ana kan nemanshi inda ya ce an baza jami’an tsaro don kamo shi.”

An kama matar da ta watsa wa mijinta man gyada mai zafi

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta kama wata mata kan zargin watsa wa mijinta tafasasshen man gyada a jihar.

Wacce ake zargin mai suna Hope ta aikata hakan ne kan wata ‘yar hatsaniya tsakaninta da mijin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel