Ni Na Hana Arewa Kamawa da Wuta, Gwamna Matawalle Ya Bayyana Dalili
- Karamin minsitan tsaro ya bayyana abin da ya yi don tabbatar da an samu tsaro a Arewacin Najeriya a lokacin da yake gwamna
- Matawalle ya ce ba don abin da ya yi ba, da yanzu Arewa ta gagari jama'a da dama, amma ya yi aiki tukuru
- A halin da ake ciki, Zamfara na daga jihohin da suka fi fuskantar matsalar ta'addanci a Arewacin Najeriya
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
FCT, Abuja - Bello Matawalle, tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya ce ba don daukar matakin da ya yi a matsayinsa na daya daga jiga-jigan jihar Arewa maso Yamma ba, da dukkanin yankin Arewa ya kama da wuta.
Matawalle, wanda shi ne karamin ministan tsaro, ya bayyana haka ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Abuja, Daily Trust ta tattaro.
Da yake bayyana rashin tsaro a matsayin babbar barazana, ministan ya ce akwai masu kasuwanci da rashin tsaro da ke yaki da kawo karshen rashin tsaro a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ake ci da ta'addanci a Arewa
Ya bayyana cewa a lokacin da yake gwamnan Zamfara, ya lura da cewa a lokacin da ake sayar da kwalbar leon Coke a kan N100 a birni, 'yan kasuwa na siyarwa 'yan bindiga a dazuka a kan kudi N500.
Ya kara da cewa:
“Haka kuma, idan ana siyar da buhun shinkafa tsakanin N18,000 zuwa N21, 000, idan ta isa ga 'yan bindiga, sai ta kai N80,000."
Su wa za su magance matsalar tsaro?
Ministan ya kuma ce, tsaro hakki ne na hadin gwiwa ga da ya rataya a wuyan kowane dan kasa, inda ya bukaci da a ajiye sabanin da ke tsakanin juna a hada kai don magance matsalar, rahoton The Cable.
Yakar Falasdinawa da Isra'ila ke yi: Ayarin farko na motocin agaji daga daular Saudiyya sun isa Gaza
Ya ce idan ba don wasu ayyukan da ya yi a matsayinsa na gwamna ba a wancan lokacin, da yanzu yankin Arewacin kasar nan ya gagari jama'a.
Daga abubuwan da ya aikata, ya ce ya datse amfani da hanyoyin sadarwa a jiharsa, wanda ya haifar da da mai ido a fannin tsaro.
Sace dalibai a Zamfara
A wani labarin, karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana yadda Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ki amsa kiran da ya yi masa.
Ya yi hakan ne a lokacin da ake tsaka da jimamin sace daliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau, lamarin da ya fi daukar hankalin al'umma.
Jihar Zamfara na daga jihohin da ke fama da yawan sace mutane, al'umma na kuka kan yanayin da ake ciki.
Asali: Legit.ng