Shahararren Dan Wasan Kwaikwayo a Arewacin Najeriya, Samanja, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Shahararren Dan Wasan Kwaikwayo a Arewacin Najeriya, Samanja, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Ana cikin jimami bayan rasuwar shahararren dan wasan kwaikwayo, Alhaji Usman Baba Pategi
  • Marigayin wanda aka fi sani da Samanja ya rasu ne a daren Asabar 11 ga watan Nuwamba a jihar Kwara
  • Samanja ya yi kaurin suna a wasan kwaikwayo da aka shafe shekaru da dama ana yi a gidan rediyon Najeriya ta Kaduna

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Shahararren dan wasan kwaikwayo, Alhaji Usman Baba Pategi ya riga mu gidan gaskiya.

Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja mazan fama ya rasu ne daren ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba bayan ya sha jinya, cewar Channels TV.

Marigayi Samanja ya rasu yana da shekaru 81 a duniya wanda ya yi suna a wasan kwaikwayo da aka shafe shekaru ana gabatarwa a gidan rediyon Najeriya da ke Kaduna.

Kara karanta wannan

Wanene Samuel Anyanwu? Abubuwa 5 game da dan takarar gwamnan PDP a jihar Imo

An haifi Samanja a ranar 20 ga watan Mayun shekarar 1942 a masarautar Pategi da ke jihar Kwara a Arewacin Najeriya, Leadership Hausa ta tattaro.

A shekarun 1960 ya shiga Rundunar Sojin Najeriya inda ya rike mukamin Kyaftin a lokacin yakin basasa, cewar PM News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a yi jana'izar marigayi a yau Lahadi 12 ga watan Nuwamba a gidansa da ke Kabala Costain a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.