Zaben Jihar Edo: Jerin Laifuffukan Zabe da Ka Iya Jefa Mutum Gidan Yari

Zaben Jihar Edo: Jerin Laifuffukan Zabe da Ka Iya Jefa Mutum Gidan Yari

  • Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta shirya tsaf domin sake gudanar da zaben gwamna a jihar Edo a ranar Asabar, 21 ga watan Satumba
  • Akwai bukatar a sake tunatar da ‘yan Najeriya dokokin da ke hana aikata laifuffukan zabe da katsalandan ga tsarin gudanar da zaben
  • Masu jefa ƙuri'a a zaben Edo ba za su tsira ba idan suka karya daya daga cikin dokokin zaben da suka hada da sayen kuri'u da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida Read

FCT, Abuja - Kamar dai yadda ya ke a sauran kasashe, Najeriya ma na da dokoki da za su daidaita tsarin zaze da kuma hana aikata laifukan zabe.

Kara karanta wannan

Zaɓen gwamna 2024: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da siyasar Edo

Aikata daya daga cikin laifukan zabe na iya jefa mutum cikin fushin 'kuliya manta sabo', gami da dauri idan har laifin ya munana.

Mayan laifuffukan zabe a Najeriya da ka iya jefa mutum gidan yari.
Sanin doka: Jerin laifuffukan zabe yayin da mutanen Edo za su fita zaben gwamna ranar Asabar. Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) za ta gudanar da zaben gwamnan Edo a ranar Asabar 21 ga watan Satumba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga wasu manyan laifuffukan zabe da hukuncinsu kamar yadda ya ke kunshe a kundin hukumar INEC.

1. Laifi a bangaren rajista

Sashe na 114 (a zuwa f) na dokar zabe, ya fitar da jerin laifukan zabe da suka shafi rijistar masu zabe.

Sun hada da rajista sau biyu, buga takardar rijista ta jabu da kwaikwayar sa hannun jami’in rajistar zabe, da dai sauransu.

Dokar kasa ta bayyana cewa wadannan laifuffuka za su iya kai ga cin tarar mutum Naira miliyan daya ko daurin watanni 12 ko kuma duka biyun.

Kara karanta wannan

PDP, APC, LP: Malami ya hango jam'iyyar da za ta lashe zaben gwamnan Edo

2. Laifi a tsaya wa takara

Sashi na 115 ya tsayu ne kan aikata laifuffukan da suka shafi tsayawa takara ga 'yan siyasa, wanda za su iya aikatawa dangane da takardun shaidar tsayawa takararsu.

Wadannan laifuffukan sun hada hada da buga takardun shaidar tsayawa takara na jabu, ko buga sakamako na jabu, yin jabun takardar kada kuri'a.

Sauran laifuffuka a wannan sashi sun hada da lalata takardun kada kuri'a, mallakar takardun kada kuri'a ba tare da suna da karfin ikon yin hakan ba, da sauran su.

Kamar yadda dokar zabe ta tanada, irin wadannan laifuffukan za su jawo a ci mutum tarar Naira miliyan 50 ko kuma zaman gidan yari na wani lokaci da bai gaza shekaru goma ba, ko kuma duka biyun.

3. Tayar da hankula a tarukan siyasa

Sashe na 116 na dokar zaben Najeriya ya yi nuni da cewa:

“Duk mutumin da a wajen taron siyasa ya aikata wani abu, ko ya ingiza wani ya yi abin da bai dace ba da nufin hana gudanar da makasudin hada taron, ko kuma yana dauke da makami ko makamai masu linzami a hannunsa; ya aikata laifi kuma za a iya yanke masa hukunci da ya hada da tarar naira dubu dari biyar ko zaman gidan yari na tsawon watanni 12 ,ko duka biyun."

Kara karanta wannan

Matasa sun shuna wa yan sanda manyan karnuka, magana ta shiga kotu

4. Karya dokar amfani da katin zabe

Sashi na 117 na dokar zabe ya yi hani da yin amfani da katunan zabe ta hanyar da ba ta dace ba.

Dokar ta ce:

“Duk mutumin da (a) ya ke da hakkin mallakar katin zabe, sannan ya bai wa wani mutum domin amfani da katin a wani zabe, in ban da jami’in da aka nada kan hakan, kuma wanda ya ke kan gudanar da aikinsa, a karkashin wannan doka.
“(b) rashin kasancewar mutum jami’in da yake gudanar da aikinsa a karkashin wannan doka, amma ya karbi wani katin zabe da sunan wani ko wasu mutane, don amfani da shi wajen zabe, ya yi hakan ne da suna aikata zamba,
"(c) ba tare da wani dalili na doka ba, ya mallaki katin zabe fiye da daya a hannunsa, ko
“(d) saye, sayarwa ko nemo katin zabe, ba kamar yadda wannan dokar ta tanadar ba, wanda ya yi hakan ya aikata laifi kuma yana da za a iya yanke masa hukuncin tarar naira miliyan daya ko daurin watanni 12, ko kuma duka biyun."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na shirin kare hakkin yan Najeriya, za ta yaki masu tauye mudu

5. Yin sojan gona da kada kuri'a

Sashi na 119 ya yi hani da duk wani yunkuri na wani wanda bai cancanci kada kuri'a ba, na yin sojan gona da sunan wani mai jefa kuri'a.

Dokar ta kuma yi kakkausan sharadi kan wanda zai jefa kuri'a a lokacin zaɓe, kuma ya sake yin sojan gona da sunan wani don sake kada kuri'a a wannan zaben.

Irin wannan laifin yana jawo a ci tarar mutum naira dubu dari biyar ko daurin watanni 12, ko duka biyun.

Sauran laiffufukan zabe

Sauran manyan laifukan zabe sun hada da dakatar da aikin zabe (Sashe na 120), cin hanci da rashawa da hada baki (Sashe na 121), da kuma dokar yin sirri wajen kada kuri'a (Sashe na 122).

Sauran sun hada da jefa kuri'a ba bisa ka'ida ba ko bayar da bayanin karya (Sashe na 123), wanda ba a yi wa rijista ya kada kuri'a (Sashe na 124).

Kara karanta wannan

Edo 2024: Jerin yan takara 17 da suke neman kujerar gwamna

Akwai kuma rashin da'a a wajen gudanar da zabe (Sashe na 125), aikata laifuffuka a ranar zabe (Sashe na 126), nuna karfin iko (Sashe na 127), barazana (Sashe na 128) da sauransu.

Jam'iyyu 9 sun goyi bayan APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu jam'iyyun siyasa tara masu rijista a Edo sun sanar da cewa sun marawa jam'iyyar APC baya a zaben gwamnan jihar na ranar Asabar.

Jam'iyyar NRM, SDP, ZLP, APM, ADP, APP, Accord, YPP da kuma AA ne suka marawa APC baya a wani taron manema labarai da suka kira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.