NLC da TUC Sun Gamu da Cikas, Kotu Ta Hana Ƙungiyoyin Kwadago Tsunduma Yajin Aiki a Najeriya

NLC da TUC Sun Gamu da Cikas, Kotu Ta Hana Ƙungiyoyin Kwadago Tsunduma Yajin Aiki a Najeriya

  • Ƙungiyoyin kwadago na kasa da sauran kawayensu sun gamu da cikas a yunkurinsu na tsunduma yajin aikin sai baba ta gani
  • Kotun ɗa'ar ma'aikata ta Najeriya ta hana ƙungiyoyin ma'aikatan shiga yajin aikin a wani hukuncin cikin shari'a da ta yanke ranar Jumu'a
  • Mai shari'a Benedict Kanyip ya ce wannan umarnin hanin zai ci gaba da aiki har sai Kotu ta yanke hukunci kan karar da ke gabanta

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun ɗa'ar ma'aikata ta Najeriya (NICN) ta hana ƙungiyoyin kwadago na ƙasa NLC da takwararta TUC shiga yajin aikin da suke tsara a faɗin ƙasar nan.

Shugaban Kotun, mai shari'a Benedict Kanyip ne ya bada wannan umarnin ranar Jumu'a, 10 ga watan Nuwamba, 2023, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun bankaɗo wani makirci da aka ƙulla, sun yi kakkausan gargaɗi kan zaben Gwamna a jihohi 3

Shugabannin kwadago na ƙasa.
NLC da TUC Sun Gamu da Cikas, Kotu Ta Hana Ƙungiyoyin Kwadago Tsunduma Yajin Aiki a Najeriya Hoto: @NLCHeadquaters
Asali: Twitter

Mai shari'a Kanyip ya yanke wannan hukuncin ne a ƙarar da Antoni Jana na tarayya (AGF) ya shigar a madadin Gwamnatin tarayyan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyoyin kwadagon sun bayyana cewa zasu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar 14 ga watan Nuwamba, 2023.

Meyasa Kotun ta ɗauki wannan matakin?

Kotun ta ƙara da bayanin cewa wannan umarnin na wucin gadi za ta ci gaba aiki har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan karar da AGF ya shigar.

A cewar alkalin, sashi na 7 (1) da na 19 (a) na kundin dokokin NICN ya ba Kotun damar sauraron irin wannan buƙata da ba da umarnin hani idan aka yi barazanar yajin aiki amma ba a tsunduma ba.

Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan mambobin NLC da TUC sun gudanar da zanga-zangar lumana a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262